Jama’a barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Taskira, Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wanda suka hadar da rayuwar yau da kullum, soyayya, zamantakewar aure da dai sauransu.
Shafin yau zai yi magana ne a kan rashin cika alkawarin saurayi ga budurwarsa, duk da cewa a can baya mun taba magana a kan cika alkawari, sai dai a yau zamu kara yin duba ne bisa alkawarin da ya shafi tsakanin masoya, musamman ta yadda wasu mazan ke kasa cika wa masoyansu alkawarin da suka daukar musu.
- Bukatar Samar Da Isasshen Taki Cikin Sauki Ga Manoma
- Malam Ina So A Taimaka Mun Da Maganin Damuwa Da Bakin Ciki?
Duk da cewa da yawan wasu matan ne ke neman bukatar hakan wajen samarin, wanda wasu sukan yi kokarin tursasa wa samarin ta yadda ko da ba za su iya ba dole ne su daukar musu alkawarin abin da suke son a siya musu.
Yayin da wasu mazan kuma su suke daukar wa kansu alkawarin ba tare da sun yi tunanin iya cika shi ba, dan su birge matan kawai, ko da kuwa mace ta nuna rashin bukatar hakan sai su tursasata da lallai sai sun siya.
Sai dai kuma akan samu akasi da rashin sa’a wajen kasa cika alkawarin da suka daukar musu, musamman idan an saka lokacin cika alkawarin, da zarar sun ga lokaci ya cika sai su fara kame-kame da kwana-kwana na karyayyaki daban-daban, gami da rashin abun fada.
Ya kamata masu irin wannan hali su daina, ga su ‘yan matan masu karbar abun hannun saurayi, da kuma mazan da suke yin alkawarin da ba za su iya cikawa ba, ba dan komai ba sai dan a tsira da mutunci da kima, a takaice kenan.
Dalilin haka wannan shafi na Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa inda suka bayyana na su ra’ayoyin kamar haka:
Zahra Abubakar (Dr. Zarah), Jihar Kano Karamar hukumar Nassarawa:
Alkawari na da muhimmanci amma a da kam. A yanzu mutane na yi wa alkawari rikon sakainar kashi an maidashi kamar ba komai bane a wannan lokaci ayi alkawari aki cikawa ba komai bane. A gaskiya mafi yawan samarin shaho wanda babu gaskiya soyyayar ma ta karya ce ba auren ne a ransu ba ba su da abun yi da ya wuce su shirga karya su dauki alkawarin abun da ba za su iya ba kuma suna cewa ba su da halin cika6 wannan alkawarin ina kira ga samarin wannan zamani da su dai na daukar wa ‘yan matansu irin wannan alkawarin na duk abun da suka san ba za su iya cika wa ba kwata-kwata ba shi da amfani hakan ba dai-dai bane. Hakan ya sha faruwa da ni an sha yi min alkawarin abubuwa da dama wanda ba a iya cika min kuma akwai halin yin hakan karya ce kurum. Hakan na jawo raini matuka da zubewar mutunci tun farko in kasan ba ka da halin cika alkawari ko wane iri ne kar ma ka dauka hakan ya fi girma da arziki matukar babu kwadayi kuma za a zauna lafiya. A Gaskiya shawarar da zan bawa masu irin wannan halayar su gyara su daina kwata-kwata hakan ba ki ma bane, domin shi fa kyan alkawari cikawa ne kuma addinin mu ma ya mana hani da daukar alkawari kuma ka saba.
Abdulazeez Yareema Shaheed (Dan Amar) Jihar Kano:
Bahaushen da ya fi cika alkawari akan na yanzu, domin na yanzu mafi akasari za su dinga alkawari suna sabawa tare da yin karya. Duk samarin da ke daukarwa mace alkawarin da sun san ba za su cika ba, to tun dama ba son tsakani da Allah suke masu ba, kuma ko da sun yi aure a karshe sai auren ya mutu idan ita budurwar ta gano cewa bai da komai sai karya, don haka mu daina karya mu kyautata iya iyawarmu. Rashin cika alkawari na jawo fitina da fada da rashin zaman lafiya a tsakanin al’umma. Ina ba da shawara da mu ji tsoron Allah, mu daina kin cika alkawari a tsakaninmu.
Nabeela Dikko daga Jihar Kebbi:
Alkawari abu ne mai muhimmanci a addinance, kafin ma aje ga al’adar Mallam Bahaushe shiyasa ‘yan Hausa kan ce “Kyaun alkawari cikawa.” Gaskiya mutanen da sun fi sanin muhimmancinsa, sannan sun fi riko da alkawari da gaske, sabanin yanzu an dauki alkawari kamar almara. Tom a ganina dai dahuwar mutum mai kosar da shi, duk kuma abin da mutum ya daukarwa kanshi, zai wahala idan ba zai iya ba, samari a daina karya a ajiye son bzambadawa sannan a nemi sana’a Tabbas hakan ya taba faruwa da ni, a baya an min alkawari an fada min abubuwa ashe duk karya ne. Hakan na janyo raini, da tsada sannan kai tsaye wannan makaryacin zai fice a ranka Shawarata don Allah samari a daina karya, ba abu ne mai kyau ba, tana sa girma ya fadi, tana kawo raini da tsana, ku dinga fadin gaskiya so na gaske baya duba kyaun jiki ko muni bare dukiya so ba ruwan shi da abin duniya, don haka a daure a daina karya da saba alkawari.
Fauziyyah S. Madaki daga Jihar Kaduna:
Mutanen da suna caukar alkawari tamkar ibada, idan har suka dauki alkawari hankalinsu ba ya kwanciya sai sun cika, sabanin mutanen yanzu da sam ba su dauki cika alkawari a bakin komai ba. Mutanen yanzu sam basa daukar alkawari da muhimmanci. Toh gaskiya sam bai dace ka sabawa da yarinya abin da ba za ka iya dorewa kana yi ba, ko da ita ta nuna tana son abu toh ka nuna ma ta ba zai samu ba ina ganin hakan zai fi, matukar soyayyar gaskiya take maka to za ta fahimce ka, amma babbar matsalane ka fara abun da ba za ka iya yi bayan aure ba. Hakan bai taba faruwa da ni ba, ni ma ban taba yi ba, ina iya kokarina wajen ganin ban karya alkawari ba. Hakan ya kan janyo rashin yarda, da kuma rashin ganin girman wanda ya karya alkawarin. Shawarata ga wanda ba sa cika alkawari su yi kokari su zama masu cika alkawari, domin cika alkawari halin manzon Allah ne, sannan cika alkawari yana karawa mutum kima da daraja.
M.Y Afrasim daga Sokoto:
Bahaushe na da yana daukar alkawari da muhimmanci kamar addini. Bahaushe na yanzu kuwa bai damu da cika alkawari ba saboda ya zubar da al’adar shi wadda tayi kaman ceceni ya da addininshi. Samari suna yin hakan ne a tunanin su idan ba su hada da karya ba ba za a so su ba. Ban taba yi wa budurwa ta alkawari na kasa cikawa ba, idan ta bukaci abin da ya fi karfi na kai tsaye zan gaya mabta bana iyawa. Wanda yayi alkawari girman shi zai fadi wadda aka yi wa kuma kunya zai shiga tsakanin su. Shawara daya ce kawai a guji karya saboda zubar da mutunci.
Hafsat Yusuf Muhammad:
Mahimmancin alkawari a gurin bahaushen da yana da alkawa sosai wallahi ba za ka sami bahaushen da ya sama maka alkawari ba gasu da kirki da zumunci, amma bahaushen yanzu akwai saba alkawari sosai maku sai dai Allah ya shirya su ya ganar da su amin. Da farko saurayi sai ya yi wa budurwasa alkawari kuma ya san ba zai iya ba ya ce zai yi kuma a karshe su sami matsala sosai dan wallahi za ta kira shi makaryaci ko kuma marowaci kuma wallahi ta raina shi har abada a karshe idan ya ce zai yi ma ta wata siyayyar wallahi ba za ta yada ba saboda sun yi ba sau daya ba, ba sau biyu ba, fatanmu Allah ya ganar da mu. Wallahi hakan bai taba faruwa da ni ba sabida abin saurayi bai dameni ba kuma wallahi ban taba cewa saurayina yayi min wani abu ba, shi ma ya sani yana alfahari da ni akan hakan kuma in sha ba zan taba cewa yayimin wani abu ba. Abin da ya ke jawo wa raini da kuma ba za ta taba ganin mutuncin ka ba kullum makaryaci ne, kai a gurinta, shawarar da zan bawa masu irin wannan su daina hakan idan kasan ba za ka yi wa yarinya abu ba sai ka fada ma ta gaskiya wallahi ba za ta ji haushi sosai ba akan yadda ka ce min za ka yi dan Allah samari ku gyara Allah ya shirya mu nagode.
Muhammad Bamalli Inkiya (Bazazzage mai Iyali):
Assalamu alaikum warahmatullah wabarka tuhu. Maganar gaskiya ada bahaushe ya dauki alkawari da matukar muhimmanci tamkar wata ibada na musamman wanda yake ganin idan har bai cika ba zai iya gamuwa da wani mummunar abu. Amma sabanin yanzu bahaushe bai dauki amana, alkawari a bakin komai ba domin wasu da yawa suna ganin kamar ita alkawari tamkar kawai a fatar baki ne da bai zama dole a cika shi ba. Tabbas hakan yana faruwa amma maganar gaskiya sau da yawa laifin ba daga samari bane, su matan ne ke dabi’antar da samari ta hanyar da za su rika yi masu karairayi.
Misali za ka ga budurwa tana tambayar saurayi kudin anko, lalle, da sauransu. Maganar gaskiya hakan bai taba faruwa da ni ba, sai dai hana karya akwai lokacin dana yi wa wata yarinya alkawari cewa idan ta aure ni zan bar ta tayi karatu a duk makarantar da take so, daga baya kuma auren ma bai yu wa, kuma wannan ai ba za a kira shi da karya ba. Maganar gaskiya da zarar saurayi ya yi wa budurwa alkawari, kuma ya kasa cika wa ko yaki cikawa abin da ke zuwa a farko shi ne rashin ganin darajar sa, domin alokacin mutuncinsa zai zube ma ta a Ido, rashin yarda, rashin girmama wa sannan daga baya kuma a fara tunanin rabuwa. Shawara ta ga samari su guje wa dauke wata hanya da za ta sa su dauki alkawarin da suka san Sam-Sam ba za su iya cikawa ba, Kuma mata ku ji tsoron Allah ku daina daura wa samari abin da kuka san ba za su iya ba, Allah ubangiji yataimake mu.