• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Gezau Babu Abun Da Ke Firgita Takarata Ta Gwamnan Gombe – Inuwa

by Khalid Idris Doya
3 years ago
Gombe

Gwamnan Jihar Gombe kuma dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya shaida cewar babu wani abun da ke firgita shi dangane da takarar kujerar gwamnan Jihar don haka shi kam ‘Ko-Gezau’.

Inuwa ya yi ikirarin cewa abokan hamayyarsa ba su wani tada masa hankali kuma ba su zama masa barazana kan neman tazarce da ya ke yi ba, domin ya san kwaf daya zai musu ya zarce lura da abun da ya kira gamsuwa da salon mulkinsa da al’ummar Gombe suka yi sakamakon kyawawan ayyukan da ya shimfida musu a zangonsa na farko.

  • Sam Yanzu Bana Jin Dadin Wannan Rayuwar, Ina Fatan Haduwa Da Allah Lafiya — Dantata

Gwamnan ya shaida hakan ne a yayin da ke ganawa da ‘yan jarida bayan gudanar da gangamin yakin neman zaben a gundumomin da suke karamar hukumar Billiri da ke jihar.

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

Gwamnan ya ce ya gudanar da ayyukan raya birane da karkara a gundumomi 114 da suke fadin jihar kuma har yanzu yana da cikakken tasiri a zukatan masu zabe wannan dalilin ne ya sanya ya ce shi kam ‘ko-gezau’ ba wata jam’iyya ko dan takarar da za ta firgita shi ko zama masa damuwa balle barazana.

“Kun gani da kanku ai, kun ga yadda dumbin jama’a ke fitowa matasa da dattawa, mazansu da mata. Dukka domin su nuna soyayya da goyon baya ga jam’iyyar APC bisa kwarin guiwar da suke da shi na cewa APC za ta iya don sun gani a kasa.

“Ina da cikakken kwarin guiwa da tabbacin za mu ci zabe. Me zai sanya na ji gezau? Ina da goyon bayan jama’a.”

A kauyen Todi, gwamnan ya yi alkawarin gina musu masallaci da coci kamar yadda al’ummar yankin suka roka. Sannan kuma zai gina hanya, makarantu da gadoji Billiri ta arewa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha
Siyasa

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump
Labarai

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Manyan Labarai

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Next Post
Yajin Aikin ASUU: Kamata Ya Yi Buhari Ya Fara La’akari Da Rahotan Briggs —Kungiyar Iyaye

Zan Yi Nesa Da Abuja Da Zarar Na Bar Mulki —Buhari

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

November 4, 2025
Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

November 4, 2025
Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

November 4, 2025
China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.