• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Jam’iyyun Adawa Na Iya Kai Bantensu A 2027?

byYusuf Shuaibu and Sulaiman
8 months ago
Jam'iyyun adawa

Tun bayan sauyin siyasa a shekarar 2015, lokacin da jam’iyyar APC ta kayar da jam’iyyar PDP shekaru biyu kacal da kafuwarta, jam’iyyun adawa a Nijeriya suke matuka fuskanci rikice-rikicen shugabanci.

Masu fashin baki dai na ganin cewa jam’iyyun adawa sun yi rauni, inda a yanzu babu wata jam’iyya za ta iya kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.

  • Gwamnatin Katsina Ta Fitar Da Naira Miliyan Dubu 50 Domin Samar Da Ruwan Sha 
  • Cece-kuce Ya Barke Kan Shirin “Kur’anic Convention”

Sun yi ikirarin cewa maimakon samar da wata gwamnati ta daban ko samar da ingantaccen bincike, jam’iyyun adawa sun shiga cikin rikicin cikin gida. Har ila yau, sun kasa gina tushe mai inganci don kalubalantar halin da ake ciki yadda ya kamata.

Hasali ma, mafi yawan manazarta na ganin cewa rashin iya zama tare na shugabannin ‘yan adawa gabanin zaben 2023 ne silar share fagen nasarar zaben Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Tun daga wancan lokaci rigingimun cikin gida a tsakanin jam’iyyun adawa sun zama ruwan dare, sakamakon batutuwan da suka hada da zaben fid da gwani, dakatar da manyan mutane, dambarwar ‘yan takara, magudi wajen zaben shugabannin jam’iyya, da hargitsa tarurruka. Jam’iyyun sun kuma fuskanci cin zarafi na kundin tsarin mulki na 1999, da dokar zabe da na jam’iyyunsu.

LABARAI MASU NASABA

ADC Ta Umarci Dukkan Mambobinta Su Yi Murabus Daga Tsoffin Jam’iyyunsu

Dage Zaben Shugabannin PDP Na Jihohi Ya Kara Ruruta Wutar Rikici A Jam’iyyar

A kwanakin baya, jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun adawa sun zargi APC da ruruta wutar rikicin da ke tsakaninsu, inda suka yi zargin cewa jam’iyya mai mulki na neman murkushe ‘yan adawa domin tabbatar da ci gaba da mulkin Shugaba Tinubu a 2027. APC ta musanta wadannan ikirari.

Tun da aka hambarar da jam’iyyar PDP, jam’iyyun adawa sun yi yunkuri da dama amma ba su samu nasara ba. Na baya-bayan nan shi ne samar da wata sabon jam’iyyar siyasa mai suna ‘The Alternatibe’, domin tabbatar da madafun iko a babban zabe na 2027. Wani tsohon dan takarar shugabancin jam’iyyar PDP na kasa, Segun Sowunmi, wanda ke tallata wannan sabuwar jam’iyyar, ya ce an kafa jam’iyyar ne saboda ‘yan Nijeriya sun gaji da tsarin siyasar da ake da su, suna kuma neman hanyar da ta dace.

Kafin wannan, a shekarar 2018, jam’iyyar PDP ta kulla kawance da wasu jam’iyyun siyasa 38, inda suka sanya mata suna ‘Coalition of United Political Parties’ (CUPP) a wani taro da aka gudanar a cibiyar Musa Yar’adua da ke Abuja. Wannan gamayyar dai ta yi nufin kayar da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC a zaben 2019. Shugabannin jam’iyyun ADC, SDP, NCP, LP, da sauran jam’iyyu da dama da suka yi rajista sun halarci taron.

Sai dai kawancen ta kasa hana Buhari sake lashe zabe, saboda rashin kokarin habaka dimokuradiyya na samun goyon bayan ‘yan Nijeriya.

A ranar 6 ga Disamba, 2023, PDP, NNPP da wasu jam’iyyun siyasa biyar suka kafa sabuwar kawance. Jam’iyyun da abin ya shafa sun hada da ADC, APM, SDP, YPP da ZLP.

Wannan sabon yunkuri mai suna ‘Coalition of Concerned Political Parties’ (CCPP), an kafa shi ne a sakatariyar jam’iyyar SDP ta kasa da ke Abuja. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci jam’iyyun adawa da su hada kai a yunkurin kwace mulki daga hannun APC.

A ranar 12 ga Disamba, 2024, jam’iyyar PRP ta tabbatar da cewa ta fara tattaunawa da jam’iyyar ADC gabanin zaben 2027.

Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Falalu Bello ya tabbatar da tattaunawar a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban ADC, Ralph Nwosu a Abuja. Bello ya jaddada cewa, “Mun fara tattaunawa. Ba ma tsoron hadewa kwata-kwata. Jam’iyyar PRP ita ce jam’iyyar siyasa mafi dadewa a yau, kuma muna da tarihin kawance da suka samu nasara.”

Ana ta rade-radin cewa za a raba madafun iko tsakanin Atiku, Kwankwaso da Obi, inda Atiku zai yi mulki na tsawon shekaru hudu, sai kuma Kwankwaso na wasu shekaru hudu, da Obi na tsawon shekaru takwas. Sai dai a kwanakin baya Kwankwaso ya musanta wanzuwar irin wannan yarjejeniya, inda ya bayyana hakan a matsayin kage.

Shi ma ya musanta wata tattaunawa na hadewa ko yarjejeniyar siyasa da PDP, NNPP ko wata jam’iyya.

Wani mai sharhi kan harkokin siyasa, Jackson Lekan Ojo, ya yi imanin cewa jam’iyyun adawa za su iya kayar da Tinubu a 2027 idan suka yi amfani da dabaru irin na APC kafin zaben 2015. Ojo ya kara da cewa akwai batutuwa da dama a karkashin wannan gwamnati da ‘yan adawa za su iya cin gajiyarsu, da suka hada da kalubalen tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, da kuma cin hanci da rashawa.

“Idan har jam’iyyun adawa suka hada kai suka mayar da hankali kan gazawar gwamnati mai ci, musamman matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin kasar, za su iya samun nasara. Abu mai muhimmancin shi ne, a zakulo dan takara mai karfi wanda zai iya hada kan ‘yan adawa tare da gabatar da sahihin zabi,” in ji Ojo.

Daraktan makarantar nazarin zamantakewar siyasa ta Abuja, Dakta Sam Amadi ya yi imanin cewa hadewar jam’iyyun adawa za ta iya yin nasara idan har shugabannin ‘yan adawa suka kuduri aniyar cimma wata manufa ta ci gaban kasa tare da ajiye muradun kashin kai.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi
Tambarin Dimokuradiyya

ADC Ta Umarci Dukkan Mambobinta Su Yi Murabus Daga Tsoffin Jam’iyyunsu

October 3, 2025
Dage Zaben Shugabannin PDP Na Jihohi Ya Kara Ruruta Wutar Rikici A Jam’iyyar
Tambarin Dimokuradiyya

Dage Zaben Shugabannin PDP Na Jihohi Ya Kara Ruruta Wutar Rikici A Jam’iyyar

October 3, 2025
Yadda Na Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Daya – Jonathan
Tambarin Dimokuradiyya

Lalacewar Tsarin Zabe Babbar Barazana Ce Ga Dorewar Dimokuradiyyar Afirka — Jonathan

September 27, 2025
Next Post
Jam’iyyar PDP Ta Janye Daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kebbi

Rikicin Shugabanci Na Barazana Ga Babban Taron Jam’iyyar PDP

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version