Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Ko Kin San.
A yau shafin na mu zai yi magana ne akan yadda wasu mata suka dauki kansu da cewa wai su sun girmi yin soyayya.
Wai sun girma ba a soyayya:
Yanzu dai bari na fara da ke uwargida: Ya kamata ki saurari duk nasihohin da zan miki, ki gode wa Allah wurin yin amfani da baiwar da ya yi miki, na kasancewa uwargida, wato komai dai yana hannunki ne har da shi kansa maigidan naki, a daidai wannan gabar in ka ji mace tana kukan yadda sitiyarin maigidan ya yi karfi, har ta kai ga cewa ba ta iya juyawa, to ta binciki kanta.
Hakika Allah S.W.T yana cewa:
“An kawata wa mutane son ababan sha’awa daga mata”.
Asali ke abar sha’awa ce ko kin yi ado ko ba ki yi ba, to me zai sa ba za ki yi adon domin ki karkato da hankalin maigidanki zuwa gare ki ba. Wasu matan su kan kalli wasan kwaikwayon Indiya sai su rika sha’awar yadda maza suke ma’amalla da matansu, wasu kuma wasu kuma wasan kwaikwayon Hausa suke kallo, to amma akwai wani abin lura, shi ne, shin mu a wannan matattarar tamu, mace ta kan kure adaka ta sha turare ga lalle yana daukar hankali, ta saka kayan da za su rika fizgar hankalin mai kallo don kawai ta yi rawa a gaban maigidanta ta tayar masa da sha’awarsa ya ji yana bukatarta.
Mai yuwuwa wani ya ce wannan al’adar Yahudu da Nasara ce, ko ita matar malam Bahaushe ta ce haba wannan ai sai yara mu mun girma ko ta ce sai kuma a ganki tsofai-tsofai da ke ga yara sun isa aure kina yi wa maigida rawa to amma kuma tana bukatar soyayyarsa.
Asshaikh Nasiruddeen Al’Albani RH ya fitar da wata fatawa a cikin majallar (Mujallatul Asaalah 8/ 74) yake cewa rawar da mace za ta yi a gaban maigidanta rawa kawai da aka saba ba wai na gaban jama’a ba (ba wai a wasan kwaikwayo da wuraren bukukuwa ba), kuma ba koyo ta yi masamman don ta rika yi ana gani ba, wannan ko da za ta motsa sha’awar maigida babu wani nassi da ya haramta, amma da sharadin cewa daga ita sai maigidanta kawai.
An tambayi malam cewa:
To in ta saka irin kayan da masu rawa a wasannin kwaikwayo suke sakawa tsaya a gaban mijinta, ashe wannan ba koyi da su take yi ba, kuma da nuna kauna ga abin da suke yi, sai ya ce “Wannan halas ne matukar a tsakankanin ma’auratan ne, kuma ba wani ba.