A farkon wanann watan ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kammala kulla yarjejeniyar daukar dan wasa Kylian Mbappe, wanda kwantaraginsa ya kare a Paris St Germain a karshen 30 ga watan Yunin wannan shekarar.
Ana sa ran dan wasan mai shekara 25 a duniya zai koma Sifaniya da buga wasa a ranar 1 ga watan Yuli da zarar an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a La Liga. Koda yake a lokacin ana tsaka da wasannin Euro 2024, kenan za a jira kwazon da tawagar Faransa za ta yi ko za ta kai wasan karshe da za a yi ranar 14 ga watan Yuli mai zuwa.
- Kakakin Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ya amsa Tambayoyin ’Yan Jaridu Game Da Sayarwa Taiwan Makamai Da Amurka Ta Yi A Sabon Zagaye
- ‘Yansanda Sun Cafke Ɗan Banga Kan Zargin Kashe Mutum 2 Kan Rikicin Gona A Adamawa
Daga nan ne Mbappe zai dauki hutu, sai kuma ya koma Real Madrid inda kungiyar ta sanar da cewa za ta gabatar da shi a gaban magoya bayanta a filin wasa na Santiago Bernabeu a ranar 16 ga watan gobe. Tun cikin watan Fabrairu dan wasan na tawagar Faransa ya amince baka da baka da cewar zai koma Real Madrid, sannan cikin watan Mayu aka sanar da zai bar PSG a karshen kakar wasa ta 2023 zuwa 2024.
Mbappe yana da shekara 16 ya fara buga wa Monaco wasa a Disambar shekarar 2015, wanda ya doke tarihin Thierry Henry a matakin matashin da ya fara yi wa kungiyar wasa.
Sannan shi ne matashin da ke kan gaba a ci wa kungiyar kwallaye a tarihi, yayin da a kakar wasa ta 2016 zuwa 2017 yana cikin ‘yan wasan Monaco da suka kai dab da karshe a Kofin Zakarun Turai.
A kuma kakar ce ya zura kwallo 15 a raga da ta kai Monaco ta lashe babban kofin gasar Ligue 1 ta Faransa sannan daga baya ya koma Paris St Germain kan kudi Yuro miliyan 180 yana da shekara 18 da haihuwa.
Tsohon dan wasan na Monaco ya lashe kofin duniya a shekarar 2018 wanda aka buga a Rasha, wanda ya zama matashi mai karancin shekaru da ya dauki kofin duniya, bayan Pele a 1958 da cin kwallo a wasan karshe.
Haka kuma Mbappe ya kai wasan karshe a gasar kofin duniya a Katar a 2022, inda Faransa ta yi rashin nasara a hannun Argentina a bugun fenariti sanann shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Faransa ta Ligue 1 da aka kammala, kuma karo shida a jere yana wannan bajintar.
Ya kuma lashe Ligue 1 karo bakwai a tarihi, wanda ke fatan daukar Kofin Zakarun Turai da kuma kyautar Ballon d’Or nan gaba sai dai kafin nan yana fatan zai taimaka wa kasar ta lashe Euro 2024 da za ta buga a Jamus a bana.
Mbappe ya lashe kofin duniya a 2018, kuma shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a PSG mai 256 a raga, tun bayan da ya koma kungiyar aro daga Monaco a shekarar 2017.
Ya amince da yarjejeniyar da za ta kare a Real Madrid zuwa karshen kakar wasa ta 2029, sannan zai dinga karbar kudi fam miliyan 12.8 a kowacce kakar wasa a Real Madrid.
Haka kuma zai karbi karin ladan Fam miliyan 128 wato na tsarabe-tsarabe da za a biya cikin shekara biyar, kuma zai rike kudin tallace-tallacensa da zai samu daga kamfanoni daban-daban.
Idan ba a manta ba Real Madrid ce ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla, sannan kuma Real Madrid ce ta dauki Kofin Zakarun Turai na bana na 15 jimilla, bayan da ta doke Borussia Dortmund 2-0 a wasan karshe a filin wasa na Wembley.