Manyan yan wasan Barcelona, Marc Casado da Inigo Martinez sun samu raunuka a wasan da Barcelona ta doke Athletico a gasar Laliga ranar Lahadi, Casado ya gamu da tsagewar ligament a gwiwarsa a karshen makon da ya gabata, kuma da alama zai yi jinyar watanni biyu, in ji masu jan ragamar gasar La Liga a ranar Talata, dan wasan mai shekaru 21, ya buga wasanni 37 a dukkan gasa a wannan kakar ga kungiyar ta Hansi Flick.
Raunin ya tilasta an cire Casado a minti na 67 na wasan da aka ci 4-2, a cikin wata sanarwa da Barcelona ta fitar ta ce “An tabbatar da cewa ya ji rauni a wani bangare na gefen gwiwarsa ta dama, za a yi masa magani wanda ke nufin da alama zai yi jinyar watanni biyu.
Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga, kuma tana fatan ganin ta lashe manyan kofuna a kakar bana duba da cewar tauraruwarsu na haskawa a halin yanzu, sannan kuma tana da wasa a hannunta, Barcelona ta buga canjaras da ci 4-4 a gasar Copa Del Rey da ta buga da Athletico Madrid a wasan kusa da na karshe.
Za su kara da Borussia Dortmund a gasar cin kofin zakarun Turai a wasan dab da na kusa da karshe a wata mai zuwa, ‘yan wasan biyu sun kare wasan da suka yi da Atlético da rauni kuma ba za su je wasannin kasa da kasa da kasar Sifaniya ba.
Nasarar da Barça ta yi a Metropolitano da Atlético Madrid ta zo da farashi yayin da Marc Casadó da Iñigo Martinez suka samu raunuka. ‘Yan wasan biyu ya kamata su kasance tare da tawagar Sifaniya don buga wasannin kasa da kasa da ke tafe amma matsalar da suke da ita na nuna cewa ba za su je wasan kasa da kasa ba.
Gwaje-gwajen da aka yi a ranar 17 ga Maris sun nuna cewa dan wasan tawagar farko Marc Casadó yana da rauni a gefen damansa, za a kara yin gwajin dan wasan don sanin girman raunin da kuma kwanakin da zai shafe ta na jinya, hakazalika Gwaje-gwaje a wannan rana kuma sun tabbatar da cewa dan wasan bayan kungiyar Iñigo Martinez yana da kumburi a gwiwarsa ta dama, za a yi wa dan wasan magani a Barcelona karkashin kulawar ma’aikatan lafiya na kungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp