A kokarin shawo kan kalubalen matsalar tsaro da ta- ki- ci ta- ki cinyewa a Nijeriya; babban hafsan hafsoshin sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa a makon jiya ya jagoranci babbar tawagar rundunar askarawan Nijeriya ziyarar musamman a Jamhuriyar Nijar domin karfafa hulda a tsakanin kasashen biyu makwabtan juna.
Ziyarar ta biyo bayan tsamin dangantakar da ta faru a dalilin barakar da ke akwai a kan sha’anin tsaro da juyin mulkin da ya kawo karshen gwamnatin farar hula ta Mohammed Bazoum a Nijar tare da hawan sojji saman mulki a watan Yuli 2023 a karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchani.
- ‘Yan Siyasar Nijeriya Ne Ke Ta’azzara Rashin Tsaro Don Cimma Wata Manufa Ta Siyasa – Shugabar WTO
- Ƙaramin Ministan Tsaro Da Manyan Shugabannin Soji Sun Isa Sokoto Domin Fatattakar ‘Yan Bindiga
Shugabannin sojojin biyu, Musa da takwaransa na Nijar, Janar Mousa Salaou Barmo sun tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaron yankin musamman kan kalubalen tsaro daga kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke fatattakar kasashen yankin Sahel wanda a kan hakan suka cimma matsayar hada hannu da karfe domin yakar su da dakile yaduwar su.
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta ECOWAS, a karkashin jagorancin shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ta yi barazanar daukar kwakkwaran matakin soji domin dawo da mulkin dimokradiyya a Nijar lamarin da ya haifar da fargaba da tsoro da nunin juna da yatsa, matakin da bai samu nasara ba wanda hakan ya bada damar zaman sulhu ta hanyar diflomasiyya domin warware rikita- rikitar da ke akwai wadda ta dauki hankalin duniya. A watan Fabrairu 2023 kungiyar ta daga takankumin da ta kakabawa Nijar kan abubuwa da dama.
A yau da sha’anin tsaro ya kara tabarbarewa, kasashen biyu sun daura damarar amfani da rundunar soji domin shawo kan matsalar. Wannan hadin guiwar muhimmi ne kansancewar sun hada bakin iyaka mai tsawon kilomita 1, 400 wadda kusan ita ce hanyar da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke amfani wajen kai farmaki.
Ziyarar Shugabannin sojojin a Nijar wani mataki ne na wata hanyar huldar diflomasiyya da kungiyar kasashen ECOWAS ta assasa domin karkarto da sauran kasashe biyu na Afrika kan su sake shiga cikin kungiyar.
A wani taro da suka yi a Abuja, babban hafsan sojojin Nijeriya wanda shine shugaban kwamitin hafsoshin tsaro na kasashen ECOWAS, ya bukaci dawowar kasashen uku a karkashin kungiyar.
Musa ya bayyana cewar dawowar kasashen uku ya zama wajibi domin yaki da matsalolin tsaro da ke addabar yankin wanda akan hakan ya ce tuni sun fara kokarin ganin kasashen uku sun dawo cikin kungiyar tare da cewar wajibi ne a hada hannu domin yaki da matsalolin tsaro a Afrika ta Yamma. Don haka a bisa ga wannan ziyarar ta makon jiya, a iya cewa ba ta rasa nasaba da kiran dawowar kasashen a cikin kungiyar ECOWAS.
Ziyarar na da manufar karfafawa shugaban gwamnatin soja a Jamhuriyar Nijar guiwa da ya sabunta alakarsa da kasashen da ke karkashin ECOWAS wadanda suka raba gari a dalilin hambarar da zababbar gwamnatin farar hula a kasar.
A watan Maris 2024, shugaba Tinubu ya bayar da umurnin sake bude bakin iyakokin Nijeriya da Nijar tare da daga takunkumin da aka sanyawa kasar da gaggawa wanda mataki ne da shugabannin kasashen ECOWAS suka dauka a wani taro a Abuja.
A jawabin manema labarai da ya sanyawa hannu, Kakakin Rundunar tsaro, Birgediya – Janar Tukur Gusau ya bayyana cewar a wajen taron dukkanin kasashen biyu sun aminta da ci-gaba da tatttaunawa da hadin guiwa wajen wanzar da zaman lafiya da magance kalubalen tsaro da karfafa hulda a tsakanin Nijeriya da Nijar.
“Sun jaddada bukatar ci-gaba da hada hannu da fadada kawance ta hanyar kai hare- haren sojoji na hadin guiwa da baiwa juna bayanan sirri da sauran dubaru. Haka ma sun aminta da kara jajircewa domin magance shigowar haramtattun makamai da karin hadin guiwa domin inganta tsaron bakin iyakokin kasashen domin dakile yaduwar makaman.”
“Haka ma bangarorin biyu sun sake jaddada matsayar su ta cewar Nijeriya kasa ce da duniya ta shaida da kyakkawar huldar makwabtaka don haka ba za ta bari a yi amfani da ita wajen kawo tayar da hankali a Nijar ba. Baya ga wannan Nijar ta aminta da sake dawowa cikin shirin wanzar da zaman lafiya a karkashin rundunar sojojin hadin guiwa ta (MNJTF)
“Haka ma hafsan sojojin Nijar, ya aminta da bukatar takwaransa da kawo ziyara a Nijeriya a inda za su kammala tattaunawa kan matakan samun nasarar hadin guiwar da suka aminta. Bugu da kari an cimma matsayar kirkirar kungiyar bayar da shawara ta Nijar wadda za ta yi aiki da takwararta ta Nijeriya da manufar magance abubuwan da suka shafi hulda da inganta sadarwa a tsakanin kasashen biyu.”
Tun da farko Musa ya bayyanawa takwaransa na Nijar a yayin da ya tarbe shi cewar sun zo ne musamman domin karfafa hadin guiwa, domin sojoji ba ‘yan siyasa ba ne aikin su shine kare kasa don haka ya ce tattaunawar su za ta kasance a kan yadda za su inganta kariyar kasashen domin Nijeriya da Nijar ‘yan uwa ne da ke hulda, aiki da karbar horo a tare a tsayin shekaru.
“Duk da yake an samu baraka a huldar mu, mun zo nan domin mu tabbatar mun ci-gaba daga inda muka tsaya. Abin da ke da muhimmanci a yanzu shine abin da ya wuce ya riga ya wuce.
“Tun safe muke tattaunawa mun kuma yi bitar duk abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabata zuwa yau. Mun yanke shawarar sake karfafa huldar da ke akwai tsakanin mu tare da komawa inda muke gabanin yau, mun yadda cewar rashin kyakkyawar sadarwa ya kara tsamin dangantaka tsakanin mu.
“Babu kiyayya a tsakanin mu, muna sane da mutanen da ke kokarin ganin sun shiga tsakanin mu, bukatar su shine su gan mu mun afkawa juna da yaki don haka ba za mu bari su yi nasarar raba mu ba. Muna son ci-gaba da aiki tare domin kasashen mu biyu su ci-gaba da samun zaman lafiya.”
“Ba za mu sa baki a sha’anin ku na cikin gida ba, haka ma ba za mu bari wasu kasashen waje su yi amfani da mu ba. Mun godewa Allah da wannan huldar. Muna tabbatarwa gwamnatin soja a Nijar da a shirye muke mu hada kai da su a kodayaushe, Nijeriya da Nijar a hade suke don haka wasu ba za su raba su ba.”
“Don haka muna rokon Gwamnatin Nijar da Chadi da ka da su bari wasu baki su shiga tsakanin mu, su guji karya da munafurci daga kowane bangare” kamar yadda fassarar tattaunawa da hafsan sojojin Nijeriya ta bayyana.
A ganawar ta musamman, hafsan hafsoshin sojojin Nijar, Janar Barmou ya bayyana bukatar da ke akwai ta kwakkwaran nazarin sha’anin tsaro ba wai domin magance matsalolin tsaron da ke akwai a yanzu ba, a’a har ma da manyan kalubalen da ke iya zuwa nan gaba.
Ya bayyana cewar yana da tabbacin ziyarar da takwarorinsa suka kawo masu za ta bude kofar kulla kyakkyawar fahimtar juna wadda za ta zama mai matukar alfanu ga hulda tsakanin sojojin kasashen biyumakwabtan juna domin tabbatar da tsaro a kasashen.
Mayar Da Rundunonin Tsaro Yankin Arewa Maso Yamma:
Masana dai sun nuna cewa mayar da Rundunonin Tsaro Yankin Arewa Maso Yamma ba zai kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da shi a kasar nan ba, suna masu cewa kamata ya yi gwamnati ta yi gaskiya ta dukufa dakile matsalar tsaro ba wai yaudara ba.
Nijeriya dai a lokacin yakin Basasa an taba tura rundunonin tsaro zuwa wani yankin Nijeriya don dakile matsalar tsaro sannan kuma an taba tura wani sashe a lokacin yakin Zangon Kataf. A wadannan lokutan, Nijeriya tana numfasawa ne bisa tsarin son zaman lafiya.
Nazeeb Sulayman Ibraheem mai sharni kan lamuran yau da kullum, ya shaida ma Wakilinmu cewa, ya ce, a lokutan baya babu kungiyoyin ta’addanci sai na kabilanci da addini.
Ya kara da cewa, yanzu kuma ayyukan kungiyoyin su ne na rashin alkibla face son zuciya da zalunci da neman abin duniya ba tare da an wahala ba.
Ya ce: “A baya, jami’an gwamnati ba su shiga shirgin fashi da makami, garkuwa da jama’a, fyade da sauransu. Burinsu kadai yankinsu. Yanzu kuma ana samun jami’an gwamnati, ‘yan siyasa da’ yan jari-hujja su na fadawa don wata bukata tasu ta son zuciya.”
“Kasantuwar wasu fitattun ‘yan kasa na sajewa da ire-iren wadannan kungiyoyin ta’addanci, zai yi wahala wannan yunkuri na tura rundunonin tsaro yankin Arewa-Maso-Yammacin kasar nan ya tasirantu. Za dai a yi ta kaiwa Dala ne ana kaiwa birni.
“Ma’ana, ana bata lokaci ne don ita kanta gwamnati ta san wadannan kungiyoyin ta’addanci ba su kadai ke sheke-ayarsu ba. Idan su kadai ne, a ina suke samun makaman zamani tun da basu ke kerawa ba?,” Nazeeb ya tambaya.
Nazeeb Sulayman Ibraheem ya daura da cewa, “Duk wani dan Nijeriya a yau ya fahimci gwamnati na shirin nan ne na bad-da-bami, in da Kulba ke barna ana cewa Kyallu ce ke yi.”
Ya kara da cewa, duk da hakan akwai mafita muddin gwamnatin tarayya za ta tashi ta yi abun da suka dace a kan lamarin, “Ra’ayi na guda daya ne kan wannan batu. Bahaushe kan ce daga kin gaskiya sai bata. To, gaskiya guda daya ce. Ba tura rundunonin tsaro ne samun nasarar shawo kan al’amarin tsaro a Nijeriya ba. A’a.
“Kawai dai gwammanti ta kama masu laifi ta hukunta su don ta san su. Bata-gari na ciki da wajenmu. Ko dai a yi abinda ya dace, ko kuwa gwamnati ta fahimci cewa ‘yan Nijeriya sun wuce a rude su da wannan tsarin don kuwa kan mage ya waye.”
Shi ma Malam Muhammad Adam, masanin tsaro ne, ya ce, “Eh idan da gaske ake yi lallai hakan zai dan rage matsalar ko da ba dukkan ba. Amma babban matsalarmu a kasar nan ba da gaske ake son kawo karshen matsalar tsaron nan ba.
“Misali, kowa shaida ne jami’an tsaronmu kwararru ne kuma masana aikinsu, to ta ina ake samun matsalar nan har yanzu ake ta kuka da kaluablen tsaro. Gaskiyar zance shine a tashi a yi abubuwan da suka kamata ba wai a tura hafsoshin tsaro na dan lokaci daga baya a sake komawa gidan jiya ba.”