Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya ce zai ci gaba da fada wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gaskiya, ko da hakan zai janyo masa kora daga jam’iyyar APC.
Ndume ya ce: “Kowa ya san abin da ke faruwa a kasar nan. Kowa yana ji a jikinsa. Kuma ba laifi ba ne in fada wa shugaban kasa don a kawo gyara”.
- Ban Ji Dadin Abin Da Libya Ta Yi Wa Super Eagles Ba – Tinubu
- Babban Yankin Kasar Sin Ba Za Ta Dakatar Da Matakai Ba, Illa Masu Neman ‘Yancin Kan Taiwan Sun Daina Matakan Takala
Sai dai ga dukkanin alamu kalaman nasa ba su yi wa jam’iyyar APC ya dadi ba, abin da ya sanya ta fitar da sanarwar yi wa Ndume gargadi.
APC ta nuna cewa Ali Ndume, babban dan jam’iyya ne kuma Sanata sannan yana da kima sosai a idonta da kuma jama’a.
Don haka ta ce bai kamata duk lokacin da za a ambace shi, sai a ce ya yi wani abu da zai tozarta jam’iyya ba.
Sanatan dai ya ci gaba da yin kiraye-kiraye don ganin Tinubu ya yi sauyi a gwamnatinsa tare saukaka al’amura ta yadda ‘yan kasa za su shaki iska.
A gefe guda ya yi suka cewar Tinubu na zagaye da gurbatattun mashawarta, wanda hakan ya sa aka kasa gane alkibilar kasar.
Idan ba a manta irin wadannan kalamai sun janyo wa Sanatan dakatarwa tare da kwace mukaminsa a majalisar dattawa, bayan da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya aike da wasika kan bukatar dakatar da shi.