Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta buga canjaras a wasan mako na 6 na wasannin neman gurbi a gasar kofin Duniya da ta buga tsakaninta da kasar Zimbabwe a Uyo.
Wasan da aka buga da misalin karfe 5 na yamma a agogon Nijeriya, ya dauki hankalin masu sha’awar kwallon kafa musamman a Nijeriya, ganin cewar Nijeriya na bukatar maki uku domin komawa matsayi na biyu a rukunin C na gasar.
- ‘Yan ta’adda Sun Kai Hari Sansanin Sojoji, Sun Kashe Uku A Borno
- Fursunoni 12 Sun Tsere Daga Gidan Yari A Jihar Kogi
Victor Osimhen ne ya jefawa Nijeriya kwallonta a ragar Zimbabwe a minti na 74 na wasan kafin Tawanda Chirewa ya farkewa bakin ana dab da tashi daga wasan, da wannan sakamakon Nijeriya ta cigaba da zama a matsayi na 4 a rukunin C.
Nasarar da Afirika Ta Kudu ta samu akan kasar Benin ya sa ta hada maki 13 a wasanni 6, kuma ta baiwa Nijeriya dake matsayi na 4 tazarar maki 6.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp