Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta lallasa abokiyar karawarta Benin da ci 4 da nema a wasan zagaye na 10 na neman tikitin zuwa gasar Kofin Duniya da suka buga a filin wasa na Godswill Akpabio dake birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.
Nijeriya ta jefa kwallayenta uku ta hannun dan wasan gaban Galatasaray Victor Osimhen, wannan nasarar ta janyo Nijeriya ta koma matsayi na biyu da maki 17 da kwallaye 6 a wasanni 10 da ta buga.
A dayan wasan da aka buga a rukunin C Afirika Ta Kudu ta samu nasarar zuwa gasar Kofin Duniya na shekarar 2026 da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da Canada bayan ta doke kasar Rwanda da ci 3-0 a Polokwane.
Nijeriya za ta jira wasa na gaba da za ta buga wanda shi ne zai tabbatar da idan za ta samu tikitin zuwa gasar Kofin Duniya ko ba za ta samu ba.