Za’a wallafa sakamakon binciken da majalisar dattawan Faransa ta gudanar game da hatsaniyar da aka samu a yayin wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai tsakanin Real Madrid da Liverpool.
Sannan ana ganin sakamakon binciken ka iya zama babbar barazana ga jami’an ‘yan sandan Faransa da kuma ministan harkokin cikin gidan kasar da ke cikin tsaka mai wuya, wato Gerald Darmanin.
‘Yan Majalisar Faransar sun tattara bayanansu daga shaidun gani da ido domin sanin hakikanin musabbabin hargitsin da aka samu gabanin soma wasan na ranar 28 ga watan Mayun da ya gabata.
Kodayake ma tuni binciken ya gano cewa, hukumomin tsaron Faransa sun gaza wajen kula da dandazon ‘yan kallo sai dai rahoton da za a wallafa ka iya musanta ikirarin ministan cikin gidan kasar wanda ya dora laifin hatsaniyar kan magoya bayan Liverpool daga Ingila.