Kasar Sin da mahukuntanta sun sha nanatawa a dandaloli da taruka daban-daban cewa, a kullum buri da manufar kasar Sin, shi ne tabbatar da ci gaba da zaman lafiyar duniya baki daya, sabanin yadda wasu kasashe ke kallonta da ma yada jita-jitar cewa, ci gaban kasar Sin, musamman kokarin da take na zamanantar da kanta, wai barazana ce ga duniya.
Har kullum kasar tana fatan kasashen yammacin duniya, musamman Amurka da sauran kawayenta, za su kalli ci gaban kasar Sin, da kokarin da take na zamanantar da kanta da ido na basira, ta yadda za su dakatar da yada farfaganda maras tushe, ta daukar wannan manufa da masu fashin baki ke cewa, za ta amfani duniya a matsayin barazana.
Sanin kowa ne cewa, hanya mafi dacewa ta warware duk wasu batutuwa da suka shafi kasashen duniya, musamman a wannan lokaci da duniya ke bukatar zaman lafiya, adalci da ma abin da al’umma za su kai ga bakin salati, ita ce tattaunawa da dukkanin kasashe masu ruwa da tsaki, maimakon ware kai, da mayar da wasu saniyar ware, da gudanar da komai a bayyane, da damawa da kowa da kowa bisa daidaito da mutunta juna, tare da ci gaba da shawarwari da hadin gwiwa, maimakon yada zarge-zarge marasa tushe.
Bugu da kari, shata layi saboda bambancin akida, da hada wata tawagar nuna wariya kan wasu kasashe, da yayata manufar ware kai tare da ’yan kanzagi, dukkaninsu sun sabawa akidun zamanin yau, kuma ba za su yi wata nasara ba. Hannu daya kuma, ba shi daukar jinka.
Ya kamata irin wadannan kasashe su san cewa, yanzu zamani ne na cude ni-in-cude ka, da martaba ka’idoji da dokoki na kasa da kasa da duniya ta amince da su, sabanin kokarin da wasu tsiraru ke yi, na nuna fin karfi ko dannayi ko, safawa saura bakin fenti, ko neman zama mai son kakabawa sauran kasashe takunkumai da ka’idojin na tilas.
Don haka, ya dace a rika martaba zabin kasashe na samun bunkasuwa, maimakon fakewa da wani batu na siyasa ko wata manufa da nufin cimma wata moriya ko neman tayar da zaune tsaye a sauran kasashe. Kowa da irin kiwon da ya karbe shi…. (Ibrahim Yaya)