A lokacin da duniya ke ci gaba ta fuskar ilimin kimiyya da fasaha, tattalin arziki, kiwon lafiya da zamantakewar Dan’adam ta fuskar tsaron rayuwa da dukiyoyin al’umma, ita kuma Nijeriya abin ba haka yake ba.
Ilimi ya zama koma-baya, wanda ilimi shi ya kamata ya zama a sahun farko a duk kasar da take son ta ciyar da al’ummarta gaba, kiwon lafiya kuma ya zamo hanyar da ‘yan siyasa ke bi don kwasar baitulmalin gwamnati a canza ta zuwa lalitar kashin kansu don son rai da rashin sanin hakin da ya rataya a wuyan su.
Idan ba a manta ba, Uwargidan Shugaban Kasar Nijeriya ta fito kafafen yada labarai ta shelanta cewa, asibitin fadar shugaban kasa babu ko sirinji ballantana a yi maganar magunguna na tsaron lafiya, kuma duk shekara ana fitar da kasafin makudan kudaden wannan asibiti.
Ta fuskar tsaro kuma ya zama wata hanya ta sace lalitar gwamnati da sunan tsaro, wanda har yanzu tsaron kullum tabarbarewa yake.
A yau muna cikin wata na hudu da sace al’ummar Nijeriya a cikin jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, ta kai matsayin da wani matashi a cikin fasinjojin da aka sace ke korafin cewa ‘yan’uwansu na son su karbo su, amma gwamnati ta hana, ita kuma gwamnatin babu wani hobbasa da take yi domin ceto su, kuma an kai wani matakin da ‘yan ta’addan ke azabtar da fasinjojin da suke tsare da su.
A Nijeriya ne kuma aka samu babban ma’ajin gwamnati wato ‘Accountant General’ da harshen Turanci da ake zargi da satar kudin gwamnati da ya kai kimanin naira biliyan 109 tare da gudunmuwar wasu daga cikin abokan aikinsa ko kuma a ce yaransa, wanda shi ma’ajin nan shi ne ummul’aba’isan shigar jami’o’in kasar nan yajin aiki, to Allah ya kyauta.
Haka kuma an samu jami’in tsaro kuma babban dan sanda mai matsayin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda a hukumar rundunar ‘yan sandan Nijeriya da ake zargi da hannu dumu-dumu a safarar muyagun kwayoyi da hada kai da muggan masu zambo cikin aminci da dukiyoyin al’umma, Allah ya kyauta.
A siyasance kuma, duk magoya bayanka idan har kai ba dan takarar da gwamnati ke goyon baya ba ne, babu kai a jerin sunayen da za a mika wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), misali kamar yadda ya kasance a Jihar Kano, duk dan takarar da ba yaron gwamna ba ne a bai samu tikitin tsayawa takara ba, wanda hakan ya zama dalilin da ya sa mafiya yawa daga cikin ‘yan jam’iyyar gwamnati sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun siyasa.
Ta fuskar ilimin jami’o’i kasar nan kuma, yau jami’o’in da suke mallakar gwamnatin Nijeriya su ne koma-baya har ta kai matsayin da sun tafi yajin aikin da babu wani da ya san yaushe za su dawo, wanda kungiyar kwadago ta gudanar da zanga-zanga, inda gwamnatin ta yi ta kokarin hana wannan zanga-zanga ya gudana amma abin ya ci tura.
Abin da mahukuntan gwamnati suke mantawa shi ne, kullum kara hura wutar bakin jini suke tsakanin jami’an gwamnati da talakawan kasar nan, an kai matakin da ko wane talaka ya san cewa gwamnatin da ya bai wa gudunmuwa ta kudi da ta jajircewa wajen ganin ta cimma nasara, yau nasarar ta samu kuma shi talaka ya zama saniyar ware a kan komai, shi ba ga noma gonakin da suka gada wajen iyaye da kakanni ba, shi ba ga kasuwanci ba, an hana shi zaman lafiya a ko’ina, babu tsaro, abinci ya yi tsada, rayuwa ta yi wahala, wanda su kuma mahukuntan kasar hankalinsu a kwance yake tamkar babu wani abu da ke faruwa, rayukan talakawa ya zama abin ko-in-kula.
Babu wanda yake damuwa don an kashe mutane a arewacin kasar nan, amma kuma idan aka kashe mutum daya a kudancin kasar nan, a lokacin ne za ka ga hankalin gwamnati ya tashi, kamar kudancin kasar nan ne kadai mutane.
A da ana matakin da sai a kan hanya ake tare mutane a yi musu fashi da makami, aka zo matakin da ake sace mutane a kudancin Nijeriya, wanda a lokacin Marigayi Sam Nda-Isaiah yake kira da babbar murya a shafinsa da yake fitowa duk ranar Litinin a Jaridar LEADERSHIP, ka da a sake a bai wa mutanen arewa damar da za su iya abin da ake kira da harshen turanci ‘Kidnapping,’ domin idan hakan ta faru abin ba zai yi kyau ba.
Amma an bar ginin tun ranar zane, yanzu mutanen arewa sun iya, kuma ya zama ruwan dare gama duniya ko’ina a arewan, babu inda ba a sace mutane ba.
Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta waiwayo talakawa ta san cewa talakawan Nijeriya sun bayar da gudunmuwar wajen kafa wannan gwamnati.