Jamhuriyar Kongo ta nemi goyon bayan Nijeriya kan ɗan takararta, Firmin Edouard Matoko, domin samun kujerar babban daraktan hukumar UNESCO. Wannan buƙata ta zo ne a yayin da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar da aniyar Nijeriya wajen ƙara karfafa dangantakar Diflomasiyya da ƙasar Kongo.
A wata ganawa da Firayim Ministan Kongo, Anatole Collinet Makosso, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, Shettima ya yaba da jagorancin Shugaba Denis Sassou-Nguesso na Kongo, musamman wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin manyan tafkunan Afirka.
- WAFU 2025: Gwamnatin Tarayya Ta Yabi Super Falcons a Matsayin Zakarun Afrika
- Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Doke Afrika Ta Kudu
Shettima ya ce Nijeriya za ta duba buƙatar da Kongo ta gabatar game da takarar Matoko, wanda ya shafe fiye da shekaru 30 yana aiki a UNESCO. Ya ce “Za mu isar da wannan buƙata ga shugaban ƙasa, kuma ina da yaƙinin cewa zai goyi bayan takarar, domin abin da ke haɗa mu ya fi abin da ke raba mu muhimmanci.”
Tun da fari, Fira Ministan na Kongo ya bayyana Matoko a matsayin gogaggen jami’i wanda ya riƙe manyan muƙamai a UNESCO, ciki har da jagorancin ofisoshin yanki da kuma matsayin mataimakin babban darakta mai kula da Afrika da hulɗa da ƙasashen waje.
Makosso ya kuma gode wa Nijeriya bisa taimakon da ake baiwa yara a Kongo ta hannun gidauniyar Rochas Foundation, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun kammala karatu, yayin da wasu ke ci gaba da karatu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp