Cibiyoyin kiwon lafiya a babban birnin tarayya Abuja sun tsaya cak yayin da likitocin da ke aiki a babban birnin tarayya Abuja suka fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku sakamakon korar ma’aikatan lafiya 127 da aka yi.
Yajin wanda aka fara a ranar Talata, ya biyo bayan cimma matsaya a wani taron gaggawa na kungiyar likitoci na cikin gida (ARD-FCTA) da ta gudanar a ranar Litinin.
- Karuwar Tafiye-Tafiye Yayin Hutun Ranar Ma’aikata A Kasar Sin Ya Bayyana Kuzarin Masu Kashe Kudi
- Zan Ba Ku $1,000 Kyauta In Zaku Koma Garuruwanku – Trump Ga Baƙin Haure
ARD-FCTA ta sanar a cikin wata sanarwa cewa, matakin tsunduma yakin aikin ya zama dole bayan da Hukumar Kula da Ma’aikata ta FCT ta rike musu albashin watan Afrilu.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta ARD-FCTA, Dokta George Ebong, da babban sakataren kungiyar, Dr. Agbor Affiong, sun yi Allah wadai da matakin da gwamnati ta dauka na cire ma’aikatan da abin ya shafa daga cikin tsarin albashi ba tare da sanarwa ko tuntuba ba, inda kungiyar ta ya bayyana matakin a matsayin “rashin gaskiya da adalci”.
A cewar kungiyar, ma’aikatan da aka kora da suka hada da likitoci, ma’aikatan jinya, masu kula da bangaren magunguna, da masana kimiyyar dakin gwaje-gwaje, an yi kuskure ne aka bayyana su a matsayin ma’aikatan bogi ko kuma wadanda basu zuwa aiki, duk kuwa da gudummawar da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukan asibiti.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp