Babbar Kotun Tarayya da ke Osogbo, a Jihar Osun, ta bayar da umarnin kama tsohon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, tare da ɗaure shi saboda ƙin bin umarninta.
Mai shari’a Adefunmilola Demi-Ajayi ce, ta bayar da wannan umarni a ranar Litinin, 29 ga watan Satumba, 2025, kafin Yakubu ya sauka daga kujerarsa a hukumance.
- Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin
- Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Kotun ta ce Yakubu ya ƙi bin hukuncin da ta bayar a baya, wanda ya umarci INEC da ta dawo da sunayen shugabannin jam’iyyar AA a shafinta na yanar gizo.
Shari’ar mai lamba FHC/OS/194/2024, wadda jam’iyyar Action Alliance ta shigar tare da wasu shugabanninta na jihohi, ƙarƙashin jagorancin Hon. Adekunle Rufai Omoaje, kan INEC da Yakubu.
Masu shigar da ƙarar sun zargi INEC da cire sunayen Omoaje da sauran shugabannin jam’iyyar daga shafinta na yanar gizo ba bisa ƙa’ida ba, duk da cewa kotu ta riga ta tabbatar da shugabancinsu a hukumance.
A yayin yanke hukuncin, kotu ta bayyana cewa: “Na farko (INEC) da na biyu (Farfesa Mahmood Yakubu) an yanke musu hukuncin tura su gidan gyaran hali saboda rashin bin hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Osogbo, Jihar Osun, ta bayar a shari’a mai lamba FHC/OS/CS/194/2024 a ranar 17 ga 5 Fabrairu, 2025.”
Kotu ta kuma umarci Sufeton ‘yansanda na ƙasa da ya kama Yakubu tare da tabbatar da fara shari’ar hukuncin raina kotu cikin kwanaki bakwai daga ranar da aka yanke hukuncin.
Bugu da ƙari, kotu ta ci tarar INEC da Yakubu Naira 100,000 domin biyan masu shigar da ƙarar saboda raina umarnin kotu.
Masu shigar da ƙarar sun haɗa da Action Alliance, Farfesa Julius Adebowale, Injiniya Olowookere Alabi, Barrista Chinwuba Zulyke, Oladele Sunday, Simon Itokwe, da Araoye Oyewole, waɗanda suka wakilci kansu da shugabannin jihohi 30 na jam’iyyar.
A halin yanzu, Farfesa Yakubu ya sauka daga kujerarsa a hukumance a ranar Talata, inda Misis May Agbamuche-Mbu, kwamishinar INEC, ta karɓi ragamar shugabancin hukumar a matsayin shugabar riƙon ƙwarya.