Wata babbar kotu ta bayar da umarnin kwace dala 899, 900 da naira miliyan 304, 490, 160. 95 da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annuti EFCC ta kwato a hannun tsohon Akanta-janar, Ahmed Idris.
Mai shari’a M. A Haasan ne ya bayar da umarnin a zaman kotun a ranar 13 ga watan Disamba, yayin da yake yanke hukunci kan karar da hukumar EFCC a Nijeriya ta shigar a gabanta.
Haka kuma kotun ta umarci da a karbe kadarori 15 mallakinsa da ke Kano da Abuja.
Kadarorin da aka bayar da umarnin a kwace sun haÉ—a da babban kantin sayar da kaya na Al-Iklas, da wasu shaguna a Ladanai, da gidajen alfarma na unguwar Daneji dukkan su da ke Kano.
Haka sai gidansa da ke Karsana a Abuja, da wani fuloti dake rukunin gidaje na Blue Fauntain shima da ke Abuja.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Ahmed Idris da karin wasu mutane, gaban kotun ne kan zargin aikata wasu laifuka 14 da ke da alaƙa da sata da halarat kuɗin haram da kiyasin su ya kai naira bilyan109. BBC Hausa