Abun al’ajabi, kotun sauraron kararrakin zabe ta tarayya ta ayyana Ministocin Kwadago a matsayin wadanda suka yi Nasara a zaben ‘Yan Majalisu da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
A watan da ya gabata ne, shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Simon Lalong a matsayin ministan kwadago da samar da ayyuka, sai kuma Nkeiruka Onyejeocha a matsayin karamar ministar kwadago da samar da ayyukan yi.
Ministoci biyun, sun fafata amma sun sha kaye a zaben kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana.
Lalong na jam’iyyar APC ya fafata a zaben Sanatan Filato ta Kudu inda Napoleon Bali na jam’iyyar PDP ya kayar da shi, ita kuma Onyejeocha ta jam’iyyar APC ta fafata a mazabar Isuikwuato/Umunneochi na majalisar wakilai ta tarayya ta kuma sha kaye a hannun Amobi Ogah na Jam’iyyar Labour (LP).
Sakamakon rashin gamsuwa da sakamakon zaben, suka garzaya kotu don neman bibiyar sakamakon da INEC ta bayyana su a matsayin marasa nasara.