Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da karar da wasu mazauna birnin suka shigar a gabanta suna neman ta hana rantsar da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu.
Yayin da yake yanke hukuncin a ranar Talata, alkalin kotun, mai shari’a Inyang Ekwo, ya umarci masu karar da kowannensu ya biya Naira miliyan 10 ga ministan shari’a kuma Atoni-Janar na kasa.
- Sin Ta Bude Ofishin Jakadanci S Kasar Honduras
- Kotu Ta Dakatar Da EFCC, ICPC, DSS Daga Tsare Sanata Yari
Masu karar dai na ikirarin cewa shugaba Bola Tinubu bai samu samu kashi 25 cikin 100 na kuri’un da aka kada a baban birnin tarayyar Abuja.
Don haka suke ganin bai cancanci zama shugaban kasar nan ba.
Mai shari’a Ekwo ya ce masu karar ba su da ‘yancin shigar da karar a kotun, yana mai cewa a gaban kotun sauraren korafe-korafen zabe ne kawai ya kamata a shigar da kasrr, a maimakon babbar kotun tarayyar da ke Abuja.
Tuni dai aka rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban kasar Nijeriya a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp