Wata babbar kotun jihar Oyo da ke zamanta a Ibadan, ta hana ‘yan majalisar dokokin jihar ci gaba da yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Rauf Olaniyan.
Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Oladiran Akintola, a ranar Laraba, ta umurci ‘yan majalisar da su dakatar da ci gaba da gudanar da bincike kan mataimakin gwamnan.
- Wata Tawagar ‘Yan PDP Sun Koma APC A Jihar Osun
- 2023: Fintiri Zai Dauki Hannatu Kadala A Mataimakiyarsa, Binani Zata Sauya Namdas Da Titsi
An rawaito cewa an bukaci Majalisar ta karanta martanin da Olaniyan ya bayar kan zargin da aka yi masa a safiyar Laraba.
Hakan ya faru ne a dai dai lokacin da kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar Talata 5 ga watan Yuli, 2022 domin sauraren karar.
Hakan ya baiwa Majalisar damar mayar da martani kan batutuwan da Mataimakin Gwamnan ya gabatar.
Daraktan kula da harkokin shari’a na Majalisar, Olabanji ne ya wakilci ‘yan majalisar, yayin da Cif Afolabi Fashanu, SAN, ya jagoranci tawagar lauyoyin Olaniyan.