A ranar Laraba ne kotun majastare da ke Iyaganku Ibadan ta daure wani matashi mai shekara 23 a duniya wata daya a gidan gyara hali bisa laifin satar tunkunyar miyar dage-dage da nama da aka kiyasta kudin ta ya kai Naira 40,000.
Alkalin kotun mai suna Maishari’a S. A Adesina ya zartar da hukuncin ne bayan da wanda ake zargin (Isaac Dumabara) ya amince da aikata laifin satar miyar dage-dagen wanda aka kiyasta kudin ya kai Naira Dubu 40 a wani gidan sayar da abinci da ke garin na Ibadan a Jihar Oyo.
Alkali kotun, Maishari’a S. A Adesina, ya zartar wa da Dumabara hukunci ne ba tare da zabin biyan tara ba.
Tun da farko, mai gabatar da kara, ASP Sikiru Ibrahim, ya bayana wa kotun cewa, Damubara ya kuma saci tukunyar gas 3, stabilayza, da kuma takalma a gidan sayar da abincin mai suna ‘Pleasure Summit Restaurant’ da ke layin Magara, Iyaganku, Ibadan.
Ya kuma kara da cewa, wanda aka yanke wa hukuncin ya kuma saci talabijin inci 42 da aka kiyasta kudin ya kai N200, 000.
Ya ce, laifin ya saba wa sashi na 390(9) na dokokin manyan laifukka na Jihar Oyo na shekara 2000.