Wata kotun Majistire da ke Illorin a ranar Alhamis ta tura wani jami’in tsaron sa-kai, Kaura Joseph dan shekara 28 a duniya gidan gyara halinka bisa zarginsa da sace kadarorin miliyan N1.8 daga cikin tsangayar koyar da ilimin Kimiyyar harhada magunguna da ke jami’ar Illorin ta jihar Kwara.
Rahoton farko-farko da ‘yan sanda suka fitar (FIR) na cewa shi dai Joseph ya shiga hannu ne bayan da abokan aikinsa ‘yan Bijilante da ke aiki a mashigar jami’ar ta biyu suka cafke shi aokacin da ke kokarin guduwa da na’urar sanyaya daki (AC).
‘Yansandan sun yi zargin cewa Wanda ake zargin da kansa ya amsa cewa ya sace na’urar sanyaya daki AC da wasu kayayyakin ciki kuwa har da na’urorin masu kwakwalwa guda hudu, injunan nika, stabilizers guda shida, Laptops da wasu muhimman kayayyakin jami’ar a watan Yunin 2022.
“Wanda ake zargin ya fada da kansa cewa yana da makullin da ke iya amfani da shi wajen shiga ofisoshin dakunan bincike da nazarin ilimi, ya kara da cewa ya sayar da dukkanin kayayyakin da ya saya da suka kai na naira miliyan 1 da digo takwas ga wani da ba san shi ba.’
Dan sanda mai shigar da kara, Abdullahi Sanni, ya bukaci kotun da ta amshi bukatunsu na shigar da kara, ya kuma roki kotun da ta hukunta shi bisa tsarin doka.
Magistrate Jumoke Bangboye ya umarci a tsare wanda ake zargin a gidan gyara halinka da ke Illorin.