Mai Shari’a A. A. Bello dake Babbar kotu mai zama a jihar Kaduna yaki bayar da belin wadanda ake tuhuma da kashe marigayi Abdulkarim dan Sanata Bala ibn Na’Allah.Â
Bello ya kuma bayar da umarni a cigaba da tsare su a gidan gyara hali, inda ya kara da cewa, wadanda ake tuhumar babu wata alamar suna fama da rashin lafiya bayan an gurfanar da su a gaban kotun.
Ya kuma sa ranar 27 ga watan Yuli don cigaba da sauraron karar.
In za a iya tunawa, wadanda kotun ke tuhuma, ana zargin su ne da yiwa Abdulkarim fashi da makamin wasu kayansa masu tsada ciki harda wayarsa Samsung da na’ura mai kwakwalwa samfarin Apple tablet da kuma motarsa kirar Lexus G5-350 2013 bayan sun caka masa Wuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp