Hukumar zabe ta kasa INEC ta kebe ranar 17 ga watan Yunin 2022 don Jam’iyyu su mika mata sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da kuma Mataimakan su.
Ta sanar da cewa, zata rufe shafinta da take amsar sunayen ‘yan takarar shugaban Kasa da misalin karfe 6 na yammacin ranar 17 ga watan Yunin 2022.
‘Yan takarar Kujerar Gwamna da na Majalisar Dokoki, za ta bude shafin daga 1 zuwa 15 ga Watan Yulin 2022.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wani taro da Kwamishinonin hukumar a ranar Alhamis a Abuja.
Mahmood ya tunatar da su cewa an kammala zabubbukan fidda gwani na dukkan jam’iyyun da za su shiga takarar zaben 2023 tun a ranar 9 ga Yuni.
ya kara da cewa INEC na bukatar jami’ai hudu na daga cikin kowace jam’iyya 18 da za su yi takara su loda sunan dan takarar su a cikin rumbun tattara sunayen.
Ya ce tuni INEC ta damka wa kowace jam’iyya lambobin dan makullin da ake bude rumbun da su domin su shiga su loda sunayen ‘yan takarar su.
“Mu na kara jaddada cewa sai sunayen ‘yan takarar da su ka yi nasarar lashe zaɓen fidda gwani bisa tsarin da Sashe na 84 na Dokar Zabe ta 2023 ne kadai za a loda sunayen su a cikin rumbun,” inji shi.