Wata babban kotun tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ta dakatar da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na neman ciyo bashin naira biliyan 10 domin aikin dasa na’urorin CCTV a Jihar.
Mai Shari’a Abdullahi Liman a ranar Juma’a ya amince da rokon kungiyoyin fararen hula da aka fi sani da ‘Kano First Forum’ (KFF), cewa dole ne a kula da matakin da ake ciki dangane basuka da suke akwai.
- Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Karyata Yin Murabus Daga Mukaminsa
- Za A Kammala Babbar Hanyar Kaduna-Zariya Cikin Wata 6 Masu Zuwa — Gwamnati
Kungiyar a ranar 27 ga watan Yuni ta shigar da kara bisa matsa kaimin Darakta-Janar na kungiyar, Dakta Yusuf Isyaka-Rabiu, inda suke adawa da matakin ciwo bashin bisa dalilin cewa ba a bi ka’idojin ciwo basukan ba.
KFF ta bakin lauyoyinsu karkashin jagorancin Badamasi Suleiman-Gandu, sun roki kotun da ta dakatar da Ganduje daga cikin sabon bashin biliyan 10 da ya ke son yi.
Sauran wadanda ake kara a wannan batun sun hada da babban Antoni-Janar na jihar, Kwamishinan kudi, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar.
Sauran su ne: Bankin Access, Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Ofishin Kula da Bashi (DMO) da Hukumar Kula da Kudi (FRC).
Mai Shari’a Abdullahi Liman, ya umarci a mika wa ma’aikatar kudi ta tarayya, ofishin kula da basuka (DMO), hukumar kula da kashe kudade ta (FRC) umarnin da kotun ta bayar na dakatar da jihar daga ciyo bashin.
KFF ta dukufa adawa da ciwo bashin ne bisa dalilinta na cewa ba a bi ka’idojin da dokokin harkalla da lamuran basuka ba.
Ranar da za a ci gaba da sauraron karar za a sanar da dukkanin bangarorin da abun ya shafa.
LEADERSHIP ta labarto cewa a ranar 15 ga watan Yuni Majalisar Dokokin Jihar, ta amince da bukatar gwamna Ganduje na ciwo bashin biliyan 10 daga bakin Access domin gudanar da aikin dasa na’urorin daukan hotuna ta CCTV.