Kotun masana’antu da ke zamanta a Abuja a ranar Litinin din da ta gabata (CCPT) ta haramtawa Kamfanin Multi-Choice Nigeria Limited kara farashin kudin kallon tashoshin DStv da Gotv da ake sa ran zai fara aiki a ranar 1 ga watan Mayu.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya rahoto cewa, kotun mai alkalai Uku karkashin jagorancin Saratu Shafi’i ta bayar da umarnin na wucin gadi ne biyo bayan wani kudiri da lauyan mai shigar da kara Festus Onifade Ejiro Awaritoma ya gabatar.
A cikin hukuncin da kotun ta yanke, kotun ta hana Multi-Choice zartar kudurin karin farashin tashoshin da zai fara aiki daga ranar Laraba 1 g watan Mayun 2024.
Talla