Kotun sauraren kararrakin zaben ‘yan majalisar tarayya da na jihohi da ke zamanta a babbar kotu mai lamba 4 a Jos, ta soke nasarar zaben cike gurbi da dan takarar jam’iyyar PDP Hon. Musa Avia Aggah, ya samu da fari a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa.
A hukuncin da kotun ta yanke karkashin mai shari’a Hope O. Ozoh, Khadi Usman Umar da mai shari’a Zainab M. Bashir ta ce masu shigar da korafin sun gamsar da ita kan kes dinsu.
- Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Ya Bukaci Matasa Su Guji Fadawa Bangar Siyasa
- Ba Gaskiya Bane Cewar Muna Kashe Biliyan 196.9 Ga Masu Juna Biyu – Badaru
Kotun ta ce Hon. Aggah bai samu mafi rinjaye na kuri’un da aka kada ba, kan hakan kotun ta ayyana Mohammadu Gwoni na jam’iyyar PRP a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa.
Kotun ta umarci hukumar zabe INEC da ta mika takarar shaidar cin zabe ga Muhammadu Adam Alkali na jam’iyyar PRP a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar 26 ga watan Fabrairun 2022.