Babbar Kotun Jihar Kano ta sake dakatar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, daga gyaran Fadar Nassarawa.
Wannan hukuncin ya biyo bayan buƙatar da Gwamnatin Jihar Kano ta shigar tare da Majalisar Masarautar Kano, suna neman kotu ta hana aikin gyaran.
- Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
- Matasa 3 Sun Shiga Hannu Kan Kashe Wani Mutum Don Mallakar Filinsa A Kano
Alkalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Dije Abdu-Aboki, ta amince da ƙarar ta wucin gadi, tana mai cewa Sarkin bai shigar da hujjar kariya ko ƙalubalantar buƙatar. Kotun ta mayar da shari’ar zuwa babbar Kotu ta 15 don ci gaba da sauraro.
Masu shigar da ƙarar sun yi iƙirarin cewa bisa dokar rushe Majalisar Masarautar Kano ta 2024, fadar ta zama mallakin Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Masarautar.
A baya kotu ta bayar da umarnin hana duk wani gyara ko rushe fadar har sai an kammala shari’ar.