Wata mata da ta samu nasarar haifar jariri a gidan gyaran hali da ke Afao Ekiti a jihar Ekiti ta samu ‘yanci walwala.
A wani hukuncin da kotun daukaka kara da ke Ado Ekiti ta yanke a ranar 31 ga watan Agusta, ta jingine hukuncin da babban kotun tarayya da ke Ado Ekiti ta yanke na daure matar a gidan yari na tsawon shekara 4 sakamakon kamata da laifin sata.
Matar wacce take dauke da juna biyu a lokacin da aka daure ta, daga baya ta samu haifar jariri a cikin gidan yarin.
Matar gwamnan jihar Ekiti, Dakta Olayemi Oyebanji, ita ce ta shiga ta fita wajen nema wa matar ‘yanci, ta kuma tabbatar da cewa za ta kula da walwalar jaririn da mahaifiyarsa.
Oyebanji tun da farko ta umarci sashin kula da jinsi da su tabbatar da samar da lauyoyin da za su daukaka kara kan shari’ar da ta kulle matar a gidan yari.
A hukuncin kotun daukaka kara da ke Ado Ekiti, ta jingine hukuncin babban kotun tarayya da ta daure matar bisa dalilin cewa kotun bata bada hurumin sauraron karar da aka yi ba akan zargin satar lura da sashi na 251 na kundun tsarin mulkin Nijeriya na 1999.