Wata babbar kotu da ke Jihar Kano, ta tabbatar da dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jami’yyar.
Mai shari’a Usman Mallam Na’Abba ne, ya dakatar da Ganduje daga shugabancin jami’yyar a ranar Laraba.
- Mun Ceto Sama Da Mutane 1000 Ba Tare Da Biyan Kudin Fansa Ba – Ribadu
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mata Da Yara, Sun Kashe Mai Unguwa A Wani Sabon Hari A Katsina
Wannan na zuwa ne bayan da shugabancin jam’iyyar APC a mazabar Ganduje, ya fitar da sanarwar dakatar da tsohon gwamnan daga shugabancin jam’iyyar a matakin kasa.
Sai dai shugabancin jam’iyyar a matakin jiha, ya yi watsi da wancan hukunci tare da dakatar da wadanda suka dakatar da Ganduje.
Idan ba a manta ba gwamnatin Kano ta sanya ranar 17 ga watan Afrilu, 2024 a matsayin ranar da za ta gurfanar da Ganduje da iyalansu da wasu kan zargin aikata almundahana da dukiyar gwamnatin jihar.
Ganduje dai na shan suka kan bidiyon dala da aka hange yana sanya wa cikin aljihun babbar riga.
Tuni gwamnan jihar na yanzu, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci hukumar EFCC ta fitar da rahoton bincikenta kan bidiyon dala da ake zargin Ganduje na karba na cin hanci da rashawa.