Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Taraba da ke zamanta a Jalingo, a ranar Asabar, ta tabbatar da Agbu Kefas na jam’iyyar PDP a matsayin halastaccen gwamnan Jihar Taraba
Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Farfesa Sani Yahaya da jam’iyyarsa ne suka garzaya kotun domin kalubalantar nasarar Kefas da PDP.
- Gwamna Uba Sani Ya Taya Kansa Murna Da Hukuncin Da Kotun Zaben Kaduna Ta Yanke
- Nijeriya Ce Kasa Ta 40 A Duniya Wajen Iya Kwallon Kafa, Cewar FIFA
Mai korafin ya je kotun ne da zargin cewa zaben gwamnan da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris cike yake da aringizun kuri’u, magudi, dangwala kuri’u fiye da kima, rashin bin dokokin zabe da INEC ba ta yi ba, tare da zargin cewa an karkatar da kuri’u da dama da NNPP ta samu zuwa ga Kefas da PDP.
Don haka ne NNPP ta bukaci kotun da ta soke nasarar Kefas tare da ayyana shi a matsayin halastaccen gwamnan Jihar ba wai Kefas ba.
Sai dai kotun Mai alkalai uku karkashin jagorancin Justice GA Sumonu, ta kori karar bisa dalilin cewa masu korafin sun gaza tabbatar da ikirarin da suke yi.
“Masu korafin sun kasa tabbatar ma wannan kotu mai daraja cikakken bayanin yadda aka yi magudi a zaben kuma da gaza bayar da dalilin menene ya sa za a ayyana dan takarar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan na ranar 18 ga watan Maris
“Tun da mai korafin ya kasa tabbatar da batun aringizun kuri’u, an kori wannan karar bisa rashin sahihanci,” kotun ta yanke.
Lauyan Farfesa Sani Yahaya ya ki cewa komai bayan hukuncin. Yayin da shi kuma gwamna Kefas ya misalta nasarar tasa a matsayin burin al’ummar jihar ne ya sake cika.
Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin kakakinsa, Emmanuel Bello, ya bukaci al’ummar jihar da su rungumi hukuncin hannun biyu-biyu, ya misalta da yin Allah ne.