A ranar laraba ne, kotun shari’ar musulunci ta bayar da umarnin a ajiye mata wasu ‘yan gida daya Saifullahi Hamisu da Mujahid Hamisu da kuma wata mai suna Hassana Surajo a gidan gyaran hali, bisa zarginsu da zakkewa wata matar aure mai suna Fatima Alhassan.Â
Wadanda kotun ke tuhuma, mazauna anguwar Bachirawa ne da ke cikin jihar Kano, inda kotun ke tuhumar su da aikata laifuka uku; hada baki da zuga da kuma zakkewa matar auren.
Dansanda mai gabatar da kararar Aliyu Abideen, ya sheda wa kotun cewa, wani mai suna Abubakar Ahmad da ke da zama a anguwar Fagge ne ya kai korafin maganar a ofis din jami’an tsaro na SCID da ke anguwar Bompai a ranar 22 ga watan disambar 2022.
Abideen ya kuma yi zargin cewa, duk dai a wannan ranar da misalin karfe 4:00 na marece, wanda kotun ke tuhuma ya hada baki inda ya shiga gidan wanda ya gabatar da korafin da ke a anguwar Dorayi a Kano, ta hanyar yin ikirarin cewa, shi dan uwa ne Fatima Alhassa.
Ya ce, a saboda hakan mai korafin ya gano cewa, Saifullahi yana zakkewa matarsa da kuma yin zance da ita ta kafar sada zumunta ta WhatsApp.
A cewarsa, shi dai Saifullahi, ya kasance saurayin Fatima kafin ta yi aure, inda kuma ya amsa laifin tuhumar da ake yi masa haka shima wanda ake tuhumar na ukun.
Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan fabrairun 2023.