Wata kotun majistire da ke garin Kafanchan ta jihar Kaduna ta bayar da umarnin a garkame wani mutum mai suna Dazuli Abubakar, bisa zargin yi wa karamar yarinya fyade.
Jami’an tsaro na Sibil defen da (NSCDC) sun gabatar da Abubakar ga ban kotu, da laifin da ya saba wa sashi na 259 na dokokin jihar na final kod.
Bayan gabatar da wanda ake zargin da sauraren bayanai, mai shari’a Michael Bawa, ya dage sauraron karar zuwa ranar 1 Nuwamba.
Bawa ya umarci dansanda mai gabatar da kara da ya mika fayil din wannan kes din ga hukumar kula da hakkin al’umma domin ci gaba da bibiyar wannan lamari.
Tun da farko dai jami’in hukumar ta NSCDC Mista Marcus Audu ya gaya wa kotu cewa, mahaifiayar yarinyar ta kawo musu rahoto ofishinsu da ke Kafanchan.
Audu ya ce, Abubakar ya kawo wadda aka yi wa ta’asar mai kimanin shekara bakwai wadda ya yaudare ta da kudi naira 200.
Abubakar ya yi wa yaron barazanar kisa, idan ya tuna masa asiri abin da ya faru.
Sai dai ya ce, an dauki yarinyar zuwa cibiyar binciken harkokin da suka shafi fyace na Salama da ke Kafanchan daga nan kuma aka mayar da ita ga jami’an tsaro na hukumar NSCDC domin ci gaba da bincike.