Wata kotun majistare da ke Iyaganku a Ibadan ta bayar da umarnin a tsare mutane 29 da ake zargin masu rajin kafa kasar Yarabawa ne, biyo bayan harin da suka kai sakatariyar Oyo.
A ranar Laraba ne aka gurfanar da mutanen saboda zargin su da hannu a harin da suka kai kan sakatariyar da kuma ofishin gwamna da bai yi nasara ba.
- Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Neman Zama Madaukakiya Tare Da Sake Waiwayar Dokokin Kasa Da Kasa
- Yadda Bayern Munich Ta Hana Arsenal Rawar Gaban Hantsi A Gasar Zakarun TuraiÂ
A baya-bayan nan ne wasu mutane da suka rufe fuskarsu suka yi dirar mikiya a sakatariyar jihar, inda suka kafa tutarsu kafin jami’an tsaro su tarwatsa su.
Mutanen wadanda ke fuskantar tuhume-tuhume bakwai kan hada baki da cin amanar kasa da kuma shiga haramtacciyar kungiya da rike makamai cikin jama’a.
Mutanen da ake zargi, har da wata matashiya da manyan mata biyar, an tsare su a gidan gyaran hali da ke Ibadan bisa umarnin babban majistare, Olabisi Ogunkanmi.
Daga bisani alkalin ya dage sauraron kara ƙarar zuwa 1 ga watan Agusta, 2024.