Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kwace Dala 49,700 daga hannun Dr. Nura Ali, tsohon Kwamishinan Zaɓe na Jihar Sokoto (REC) a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a Jihar Sokoto, zuwa ga asusun Gwamnatin Tarayya.
Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, Mai Shari’a Emeka Nwite ya yanke hukuncin cewa Hukumar yaki da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta da Sauran Laifuka (ICPC) ta cika dukkan sharuɗɗan doka na kwace dalolin har abada, saboda babu wani ko wata da suka nuna kin amincewa da hujjojin da hukumar ta bayar.
- Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci
- An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe
“Na saurari bayanin da lauya mai shigar da kara ya gabatar kuma na yi nazari sosai kan hujjojin da ya gabatar. Na gamsu cewa, buƙatarsa ta cancanci amincewa. Saboda haka, an amince da ita,” in ji Mai Shari’a Nwite.
Lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya gabatar da ƙarar neman a kwace kuɗin, yana sanar da kotun cewa, ICPC ta bi umarnin wucin gadi na kwace dalolin da ta yi a baya. Ya ce, an buga sanarwa ta jama’a inda aka gayyaci duk wani mutum wanda yake ganin akwai dalilin da zai hana ko kuma bai kamata a kwace kudin ba har abada, amma babu wanda ya amsa.
“Saboda haka, muna neman a ba da umarnin a kwace kudin har abada a mayar da su ga Gwamnatin Tarayya, saboda bin umarnin wucin gadi kuma babu wanda ya nuna adawa da hukuncin,” in ji Akponimisingha ga kotun.
Hukuncin ya biyo bayan umarnin wucin gadi da kotun ta bayar a ranar 30 ga Disamba, 2024, domin amsa bukatar da ICPC da Ma’aikatar tsaron farin kaya ta cikin gida (DSS) suka gabatar tare.
Takardar neman izinin, mai lamba FHC/ABJ/CS/1846/2024, kuma Usman Dauda, Daraktan Ayyukan Shari’a na DSS ya sanya wa hannu, ta nuna cewa an gano kudaden ne a lokacin bincike a gidan Dr. Ali da ke Kano.














