Babbar kotun tarayya da ke Legas ta umarci gwamnatin tarayya da ta kayyade farashin kayayyakin masarufi da na man fetur cikin kwanaki bakwai.
Mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa ne ya ba da wannan umarnin a ranar Talata a yayin da yake yanke hukunci a cikin wata kara mai lamba FHC/L/CS/869/2023 da mai rajin kare hakkin bil’adama, Mista Femi Falana ya shigar a gaban kotun kan kula da farashin kayayyaki.
- Zanga-zangar Minna: Shugaba Tinubu Ya Ba Da Umarnin A Sassauta Farashin Kayan Abinci – Idris
- An Hada Rukunin Karshe Na Tashar Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ta Gina A Uganda Da Layin Wutar Lantarki Na Kasa
Da yake mayar da martani, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Kamarudeen Ogundele, ya ce, “Da zarar mun samu kwafin hukuncin, za mu yi nazari a kai.
“A karshe dai, dole za mu dauki matakin da zai dace da kasarmu.
“Mun tabbata cewa, wannan gwamnatin, a koda yaushe muradin talakawa ne a tare da ita.”