Hukumar samar da wutar lantarki ta kasar Uganda (UEGC) ta bayyana cewa, an yi nasarar kaddamar da rukunin karshe, na injununa guda shida dake tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Karuma da kasar Sin ta gina, inda aka hada su da tashar samar da wutan lantarki ta kasar.
A cewar hukumar ta UEGCL, wannan ya kasance rukuni na shida kuma na ƙarshe na injunan samar da wutar lantarki da za a yi amfani da su wajen samar da wutar lantarki a kasar.
- Bikin Bazara Da Ke Fadada A Duniya Alama Ce Ta Mu’amala Da Fahimtar Juna Tsakanin Wayewar Kan Kasar Sin Da Wayewar Kai Daban-Daban
- Kasar Sin Ta Taya Nangolo Mbumba Murnar Zama Sabon Shugaban Namibia
Kamfanin samar da wutar lantarkin ya ce, a ranar 21 ga watan Maris din shekarar 2023 ne, aka kammala gwajin rukunin farko na tashar da ma gwajin hada shi da babbar tashar samar da wutar lantarkin kasar.
A cewar ma’aikatar kula da makamashin kasar, ana sa ran babbar tashar samar da wutar lantarkin da aka gina a sarari da kuma kasan kogin Nilu dake arewacin Uganda, za ta samar da wutan da ya kai Megawatts 600, inda kowane inji yake samar da wutan da ya kai megawatts 100.
Karuma ita ce tashar samar da wutar lantarki ta biyu da kasar Sin ta samar da kudin ginawa, bayan tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatts 183 ta Isimba da aka kaddamar a shekarar 2019. (Ibrahim Yaya)