Wata babbar kotun Jihar Ribas da ke zamanta a Fatakwal ta yanke hukunci kan wata kara da aka shigar da jaridar ThisDay, inda kotun ta umarce ta da ta bai wa Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike Naira miliyan 200.
An bukaci ta biya kudin ne don rage masa radadin bata suna da suka yi masa.
- Dan Takarar APC Ya Kada Sanata Mai Ci A Bauchi Ta Kudu
- INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Sanatan Zamfara Ta Tsakiya Bai Kammala Ba
Wadanda ake kara a shari’ar mai lamba alama No. PHC/1505/CS/2020 sun nemi kamfanin buga jaridar Thisday, Leaders and Company Limited, Davidson Iriekpan, Chuks Okocha da Adibe Emenyonu.
ThisDay dai ta wallafa wata mukala mai taken: “With a Friend Like Wike, Obaseki Meets His PDP’s Waterloo; Almost …” lamarin da ya sanya gwamna Wike garzaya wa kotu domin neman diyyar bata masa kan biliyan bakwai a kan jaridar da ma’aikatansa uku.
A cikin karar, Wike ya yi ikirarin cewa bugun jaridar ta ranar 23 ga Yuni, 2020 an yi ne da niyyar bata masa mutunci da kima; nuna shi a matsayin mayaudari kuma marar amana, wanda shi kuma bai lamunta ba.
Da yake yanke hukuncin a ranar Litinin, Mai Shari’a Adolphus Enebeli, ya gano cewa jaridar ta aikata laifin cin mutunci da bata sunan gwamna Wike.
Alkalin ya ce ta kowace fuska, wallafar jaridar ThisDay ta ranar 23 ga watan Yuni na shekarar 2020 ta kafarta na yanar gizo ta bata kima, da kauce wa ka’idar aiki wajen bata wa mai kara mutunci.
Alkalin ya ce kasancewar jaridar ThisDay da ta dauki tsawon shekaru tana gudanar da aikinta na labarai, bai kamata ta yi sake wajen barin ‘yan bunbutun ‘yan jarida su yi amfani da kafar wajen wallafa irin wannan mukalar ba.