Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) daga kawo karshen rajistar masu zabe a ranar 30 ga watan Yuni, 2022.
Mai shari’a Mobolaji Olajuwon a ranar Litinin ya ba da umarnin cigaba da rajistar ta wucin gadi biyo bayan sauraron karar da kungiyar SERAP ta shigar a kan kudirin INEC na dakatar da rajistar.
A farkon watan yunin 2022 ne SERAP da wasu ‘yan Nijeriya 185 suka shigar da hukumar INEC kara a gaban Kotu, inda suka bukaci kotun da ta dakatar da Hukumar kan Kudirin ta na kawo karshen sabuwar rajistar masu kada Kuri’a, acewar SERAP yin hakan ya sabawa dokar kundin tsarin mulkin kasa, kuma hukumar tana son dakile wa ‘yan kasa damar gudanar da ‘yancinsu.
Kotun da dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Yuni 2022.