A’ummar garin Fadere na Qaramar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna sun tsinci kansu cikin wani yanayi na razani sakamakon fashewar Tukunyar gas din wani Mai Shayi da ya yi sanadin Kone mutum 23.
Lamarin ya faru ada yamma,. Da yake yi wa manema labarai Karin bayani kan yadda amarin ya faru, mai shayin wanda Shima bayansa da fuskarsa suka kone a sanadiyyar gobarar, ya ce mantawa ya Yi bai daure bakin tukunyar gas din ba bayan an dura masa gas. Da ya dawo ya ga an daure, bayan ya kunna wuta sai ya ga akwai matsala ashe ba su daure daidai ba.
Hakan a cewarsa ta sa ya sakko da tukunyar kasa domin ya kwance, ya sa kaga yai-yai ya kwance kada.
Ya ce; “Ina cikin kwancewa sai ya bugo murfin gas din sai iskar gas din ta fara fita waje. To da na ga ta tsagaita sai na sake shigowa don na fitar da tukunyar waje, kawai sai na ji yif kamar an kama ni kawai sai na ga wuta ta tashi ta kama kayan jikina baki daya.
Sai na fito da gudu ina kiran jama’a su cire min kayan jikina, aka samu aka kashe min,” in ji Mai shayin.
Ya ce yana amfani da gas din ne wajen soya kwai da Indimie .
” Gaskiya na yi matukar fahin ciki da faruwar wannan abin don ban so ya faru a shagona ba, amma haka Allah ya so Kuma babu yadda zan yi.
Na je Shan shayi abin ya rutsa da ni
Shi ma da yake zantawa da manema labarai, wanda ya je Shan shayi abin ya rutsa da shi, Kuma yake kwance a babban asibitin garin Saminaka, Malam Lawal Ali, ya e shi bayan ya sha shayi a shagon ya fita bakin hanya sai ya hadu da dan uwarsa inda Suka tsaya suna magana, sai muka ga Mai Shayi fadi ta baya yana dungure, sai muka ga hayaki na tashi sama.
Mun ruga za mu je sai muka ga wani hayakin ya buge mu ashe rigata ce ta kama da wuta, sai muka ruga da gudu muna Salati, sai Wani ya zo ya taimake ni muka cire rigar aka Kai ni asibiti.
Mutum 23 ne Suka kone – Dagacin Lere
A cewar Dagacin Fadere Umar Babangida Ubale, mutum 23 ne Suka kone, a cwarsa wajen da rumfar Mai shayin take kasuwa ce yara suna sayar da abinci, “Abin takaici maimakon su gudu sai Suka tsaya kallon me yake faruwa, sai silindar ta yi bindiga Kuma iskar gas din ta watsu ta kine duk mutanen da suke wurin,” in ji shi