Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutane biyu da aka samu da laifin kashe wani malami na jami’ar Northwest University a lokacin wani harin fashi da makami da ya faru a shekarar 2016.
Mai shari’a Fatima Adamu, wadda ta yanke hukuncin a ranar Litinin, ta samu Aliyu Hussaini daga Sheka Sabuwar Abuja Quarters da Amir Zakariyya daga Unguwar Malam Quarters, duka na ƙaramar hukumar Kumbotso, da laifuka uku — haɗa baki, da fashi da makami da kuma kisa da gangan.
- Atletico Madrid Ta Zazzaga Wa Real Madrid Ƙwallaye 5 A Metropolitano
- Kotu Ta Ɗaure Mai Horas Da ‘Yan Wasa Shekaru 8 Sakamakon Zargin Luwaɗi Da Ƙaramin Yaro A Kano
A cewar Alƙaliyar, “Aiyukan waɗanda ake tuhuma sun nuna rashin daraja ga rayuwar ɗan Adam.” Daga nan ta yanke musu shekaru biyar a gidan yari saboda haɗa baki, da shekaru goma saboda fashi da makami, sannan hukuncin kisa ta rataya saboda kisan kai.
Lauyan gwamnati, Lamido Abba-Sorondinki, ya bayyana cewa waɗanda aka yanke wa hukuncin sun kai hari gidan Buhari Imam, malamin jami’a, a ranar 11 ga Yuni, 2016, inda suka sace wayarsa sannan suka soka masa wuka sau da dama a ciki, da cinyoyinsa da kuma bayansa har ya ta kai ya rasu.
Kotu ta tabbatar da hukuncin ne bayan gabatar da shaida uku, da kuma rahotannin likita da hotunan mamacin, inda ta tabbatar cewa gwamnati ta tabbatar da laifin bisa shaidar da ba ta da shakku. Wannan hukunci ya yi daidai da tanade-tanaden sashi na 97(1), 298(c), da 221(a) na dokar Penal Code ta jihar Kano.