Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da ke unguwar Sharada a Kano, ta yanke wa wasu ‘yan daudu takwas hukuncin daurin watanni uku a gidan yari tare da zabin biyan tara.
Hukuncin da aka yanke wa abin ya shafa ya biyo bayan amincewa da laifin da aka karanta musu a lokacin da aka gurfanar da su a gaban kotun Hisbah.
- Kwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Ethiopia Da Ci 4 A Abuja
- Sashen Dawowa Na Kumbon Shenzhou-16 Ya Dawo Duniyarmu Lami Lafiya
Alkalin kotun, Khadi Tanimu-Sani, ya yanke hukuncin cewa kowannen su za a yi masa bulala 10, sannan kowannen su ya biya tarar Naira 20,000 tare da gabatar da mutum daya a matsayin wakili ko kuma a daure shi a gidan gyaran hali na tsawon watanni uku.
Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne jami’an hukumar Hisbah suka kama wasu mutane takwas da ake zargin ‘yan daudu ne a wani daurin aure a Kofar Waika da ke karamar hukumar Gwale a jihar.
Mataimakin babban kwamandan hukumar, Mujaheed Aminudeen Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Talata.
Rahotannin sun ce an kama wadanda ake zargin ne bisa bayanai da aka samu.
Da samun labarin jami’an Hisbah suka isa wurin ba tare da bata lokaci ba, inda suka cafke wasu takwas sanye da kayan mata suna rawar badala.