Wata babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Halima Sulaiman ta samu wata matar aure mai suna Rukayya Abubakar da laifin kashe dan kishiyarta.
Kotun ta yanke wa Rukayya Abubakar hukuncin daurin rrai-da-rai a gidan yari.
- Masu garkuwa Sun Rage Farashin Kuɗin Fansar Matar Sarki Bayan Sun Kashe Sarkin A Kwara
- APC Ta Lashe Zaɓen Mazaɓar Ɗan Majalisar Tarayya Ta Kachia/Kagarko A Zaɓen Cike-gurbi
Lauya mai shigar da kara, Barista Rabia Sa’ad, ta sanar da kotun cewa, a shekarar 2021, Rukayya ta jefa dan kishiyarta cikin rijiya, wanda hakan ya kai ga mutuwarsa.
A cewar Barista Rabia, wannan laifin ya sabawa sashe na 221 na kundin tsarin laifuffuka.
A yayin shari’ar, lauyar mai gabatar da kara ta gabatar da shaidu hudu a gaban kotun.