Wata babbar kotun da ke Abuja, ta yi watsi da bukatar da Abba Kyari ya nema kotu ta yi watsi da tuhumar da hukumar NDLEA ke yi masa kan safarar miyagun kwayoyi.
A zaman da kotu ta yi mai shari’a Emeka Nwite, ya bayyana cewa, kotun na da hurumin sauraraon kararrakin da suka shafi ta’amali da miyagun kwayoyi a tsarin milkin kasar nan da kuma dokokin hukumar NDLEA.
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Daina Muzgunawa Kamfanonin Waje
- ‘Yan Nijeriya Sama Da Mutane 39 Ne Suka Mutu A Zaben 2023
Kamfanin dillancin labarai na nijeriya, ya ruwaito cewa, ranar 18, ga watan Janairu, Mai shari’a Nwite ya dage sauraraon karar da aka shigar da Kyari da wasu mutum uku kan safarar miyagun kwayoyi.
Wadanda suka mika bukatar su ne Kyari, ACP Sunday Ubia da Insifeto Simon Agirigba da kuma Insp John Nuhu.
Wadanda ake tuhumar dai sun roki kotu da ta dakatar da tuhumar da take yi musu su bari hukumar ‘yansanda ta bincike su.
Sun ce hukumar NDLEA na da hurumin da za ta hukunta su, ba tare da sai kotu ta tuhume sub a.
Sai dai lauyan hukumar ta NDLEA Mrista Joseph Sunday, ya soki wannan bukata ta wadanda ake tuhumar.
Ya musanta cewa, ma fi yawan laifun da ake tuhuma ba su da dangantaka da dokokin aikin dansanda.
Ya bagabatar da wadanda ake tuhumar, ta hanyar mika bukatarsu a rubuce cikin wasu tasararrun bayanai.
Saboda haka Sunday ya roki kotun ta yi watsi da wannan tygyma da ake yi musu.
Da yake yanke hukunci, mai shari’a Nwite ya ce, ikon da hukumar ‘yansanda ke da shi bai wuce na babbar kotun gwamnatin tarayya ba. Ya ce, dole kotu da tsaya a iya huruminta.
Kamar yadda mai shari’a ya nuna, sashi na 251(2)(F) da (3) na tsarin milkin kasar nan ya tabbatar wa da da kotu su saurari kara kuma su yanke hukunci a kan laifin da aka yi.
In za aiya tuna wa ranar 5 ga watan Satunba, 2022, NDLEA ta gabatar da kara gaban babbar kotun gwamnatin tarayya tana.