A yau Alhamis 21, ga watan Disambar 2023, Kotun kolin Nijeriya da ke Abuja ta fara sauraren karar zaben gwamnan Kano da Gwamna Abba Kabiru Yusuf da Jam’iyyar NNPP da INEC suka shigar gabanta.
Ma su shigar da karar suna kalubalantar hukuncin kotun sauraren karar zaben gwamnan Kano da Kotun daukaka kara suka ayyana dan takarar Jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kori Gwamna Abba Gida-Gida Ta Tabbatar Da Nasarar Gawuna
- Kotu Ta Kori Karar Abba K. Yusuf Ta Tabbatar Da Hukuncin Kotun Zabe Da Ya Tabbatar Da Gawuna
A zaman na yau, tunda farko Kotun ta ce, ba ta da lokacin sauraren ƙarar NNPP da Abba da INEC da suka shigar gabanta har guda tara (9), sai dai su zaɓi guda ɗaya acikin taran.
Daga bisani kotun ta ba ma su ƙara da wanɗanda ake ƙara minti 10 kan kowane bangare ya faɗi matsayarsa. Lauyoyin APC da NNPP duka sun gabatar da jawabansu a gaban kotu.
A nasa jawabin Lauyan INEC, ya gabatar da bayyanai kan tanadin da dokar zaɓe ta yi kan kuri’un zaɓe marasa satamfi da sa-hannu da kwanan wata.
Yayin zaman shari’ar na yau Kotu ta gamsu takardun shari’a na kotun ɗaukaka ƙara na farko cewa kuskure ne, ta kuma karɓi takardu na biyu bayan da kotun ta gyara kuskuren da ke jiki.
Cikin tambayoyin da Kotu ta yi wa Lauyan hukumar zabe ta INEC ta tambaye shi shin ko waɗannan ƙuri’un zaɓen naku ne (Marasa satamfi da sa-hannu da kwanan wata)? Sai Lauyan INEC ya amsa da Eh ƙuri’unmu ne (bana bogi bane).
Daga bisani Kotu ta yi ƙarin haske kan batun satar ƙuri’un zaɓe a Nijeriya, wanda ta ce wajibi ne doka ta yi aiki don magance matsalar ba a iya Kano kaɗai ba a duk faɗin Nijeriya, saboda wajibi ne kiyaye doka da oda.
A karshe Kotun ta kammala sauraron ƙarar, ta kuma ce za ta sanar da ranar yanke hukunci kan shari’ar.