Kotun kolin ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Aminu Bande, suka shigar na bukatar tsige Gwamna Nasir Idris a matsayin gwamnan jihar Kebbi.
Kotun kolin a hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, ta ce karar d jam’iyyar ta shigar ba ta da wani inganci.
- Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Zaɓen Sule A Matsayin Gwamnan Nasarawa
- Kotun Ƙoli Ta Sake Tabbatar Da Zaɓen Abiodun A Matsayin Gwamnan Ogun
Uwani Abba-Aji, wanda ta karanto hukuncin da kotun ta yanke, ta ce: “Wannan karar ba ta da wani inganci don haka ta yi watsi da ita.”
A watan Maris na 2023, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana zaben gwamnan jihar Kebbi a matsayin wanda bai kammalu ba saboda matsalolin zabe da aka samu a kananan hukumomi 20 daga cikin 21 na jihar.
Daga baya hukumar zabe ta tsayar da ranar 15 ga Afrilu, 2023 don sake gudanar da zaben.
Inda Gwamna Idris na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 409,225 inda ya doke Aminu Bande na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 360,940.
Bande da jam’iyyarsa sun yi watsi da sakamakon inda suka shigar da kara a gaban kotun.