Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yanke a baya, wanda ya amince da matakin Gwamnatin Jihar Kano na soke Dokar Masarautar jihar ta 2019.
Wannan dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci na ƙarshe kan batun.
- Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta Ware Mata – Bincike
- Hajjin Bana: NAHCON Za Ta Fara Jigilar Maniyyata A Ranar 6 Ga Mayu
Kwamitin alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Okon Abang ya yanke hukunci a ranar Juma’a cewa ba za a ɗauki wani mataki ba a halin yanzu, don kiyaye yadda abubuwa suke.
A baya, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta rushe hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Kano na ranar 20 ga watan Yuni, 2024, wanda ya soke matakin Gwamnatin Kano na rushe masarautun jihar guda biyar tare da mayar da Muhammadu Sanusi II matsayin Sarkin Kano na 16.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin yanke hukunci kan wannan batu, domin batun sarauta yana ƙarƙashin ikon Kotun Jiha.
Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi (Sarkin Dawaki Babba) bai gamsu da wannan hukunci ba, don haka ya shigar da ƙara yana neman a dakatar da aiwatar da hukuncin har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci.
Ya shigar da Gwamnatin Jihar Kano, Kakakin Majalisar Dokokin Jiha, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Hukumar NSCDC, da sauran hukumomin tsaro ƙara.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta amince da buƙatar Dan Agundi, inda ta ce akwai hurumin shari’a a cikin ƙarar.
Mai shari’a Abang ya bayyana cewa kotu dole ne ta yi adalci wajen yanke hukunci.
Wannan hukunci yana nufin cewa dole ne dukkan ɓangarorin su ci gaba da zama yadda suke kafin Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci.
Bugu da ƙari, kotu ta umarci Dan Agundi da ya bayar da tabbacin shari’a cikin kwanaki 14, inda zai ɗauki alhakin duk wata asarar da za ta iya tasowa idan aka samu cewa dakatarwar ba ta da amfani a nan gaba.
Har yanzu rikicin masarautar Kano bai ƙare ba, kuma ana jiran Kotun Ƙoli ta yanke hukunci na ƙarshe kan lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp