Kotun ɗaukaka kara dake babban birnin tarayya Abuja, ta rushe hukuncin babbar kotun tarayya ta Kano kan zaben kananan Hukumomin jihar Kano.
Da yake karanta hukunci, mai sharia Oyewumi ya ce tun da farko babbar kotun tarayya bata da hurumin sauraron ƙara kan batun, bare har ta yi hukunci.
- Gwamnatin Kano Ta Fara Biyan Tsoffin Kansiloli Na APC Sama Da Naira Biliyan 16
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 41 Da Ake Zargi Da Kisan DPO A Kano
Saboda haka kotun ta amince da bukatar waɗanda suka daukaka kara wato bangaren gwamnatin Kano kuma ta tabbatar da zaɓen da cewa an gudanar da shi bisa doka.
A watan Oktoban shekarar 2024 ne LEADERSHIP Hausa ta kawo muku rahoton cewa jam’iyyar adawa ta APC a jihar Kano ta shigar da ƙarar gwamnatin NNPP ta jihar Kano bisa gudanar da zaɓen.
A cikin ƙarar, jam’iyyar APC ta buƙaci kotu ta dakatar da gudanar da zaɓen na kananan hukumomi, inda take zargin shugaban hukumar zaɓen ta Kano, Farfesa Sani Lawal Malumfashi da wasu ma’aikatan hukumar cikakkun ƴan jam’iyyar NNPP ne saboda haka ba su cancanta su shirya zaɓen ba.
Sai dai kwanaki uku kafin zaben mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya ya rushe shugabancin hukumar zaɓen tare da dakatar da su wajen shirya zaɓen.
Sai dai duk da hukuncin da kotun ta bayar, hukumar zaɓen ta shirya zaɓe a ranar 26 ga watan Oktoba na shekarar 2024.
Sai dai tun a wancan lokacin jam’iyyar APC ta yi fatali da zaɓen, inda ta bayyana shi a matsayin wanda bai inganta ba sakamakon saɓawa hukuncin kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp