Wata kotu a Birtaniya, ta umarci Bhadresh Gohil, lauyan tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori da ya biya tarar Fam miliyan 28 bisa taimaka wa da ya yi na boye kudaden da ya samu ta haramtacciyar hanya.
Gohil wanda dan kasar Indiya ne, kotun ta yanke masa hukuncin dauri a 2010 kan tukume-tuhume 13 na yin safarar kudade ta haramtacciyar hanya da da kuma aikata sauran laifukan da ke da nasaba da taimakawa Ibori na boye haramtattun kudade.
- NLC Ta Bai Wa Tinubu Kwanaki 7 Don Dawo Da Tallafin Mai, Ko Ta Shiga Yajin Aiki
- Likitoci Masu Sanin Makamar Aiki Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani
Ibori, ya shugabanci jihar Delta ne, daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2007.
Kazalika, kotun a zamanta na jiya Litinin ta umarci Gohil da ya biya tarar sama da Fam miliyan 28, kuma zai kara fuskantar wani daurin na shekara shida.
Kafar yada labarai ta Reuters, a jiya Litinin ta kafa hujjarta ne da sanarwar da ta samu daga ofishin yanke hukunci na CPS na Birtaniya.
Kotun dai, ta yanke Gohil hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 ne a 2010, wanda ya yi zaman rabin hukuncin, a gidan yari.
Kotun ta dauki wannan matakin ne, bayan ta yanke wa Ibori hukuncin dauri kan safarar haramtattun miliyoyin kudade a Birtaniya da wasu wuraren, inda kuma kotun a ranar Juma’ar da ta wuce, ta umarce shi da ya biya tarar Fam miliyan 101.5 wanda ya yi daidai da dala miliyan 130, ko kuma ya kara fuskantar wani hukuncin dauri na shekaru takwas.
Sai dai, a ranar Juma’ar, Ibori ya lashi takobin daukaka kara kan wannan hukunci, wanda aka yanke masa.
Bisa ga bayanan da kafar yada labarai ta Reuters samu daga ofishin CPS da ke a Birtaniya a karkashin dokar samun bayanai, bayan da Birtaniya ta karfafa dokar aikata manyan laifuka a shekarar 2002, laifin kwace kayan Ibori shi ne mafi girma na biyu, inda kuma na lauyansa Gohil ya kasance mafi girma na biyar.