Wata kotun daukaka kara da ke da zamanta Abuja, ta dage sauraren shari’ar da ‘yar takarar jam’iyyar APC Aishatu Dahiru Ahmad Binani, ta daukaka, biyo bayan hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben kujerar gwamna da bai mata dadi ba.
Kotun ta sanar da cewa ta dage zaman sauraren daukaka karar da Aishatu Binani ta shigar tana mai kalubalantar INEC, gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, da jam’iyyar PDP, da dama ranar Juma’a 1 ga watan 12 Disamba 2023, ta sanar za ta yi.
- Allah Ya Girmama Annabi (SAW) Cikin Fadi Da Aikatawa
- Shari’ar Zaben Gwamnoni: Kallo Ya Koma Kotun Koli
Da ma dai ranar da kotun ta sanar na cikin wata takardar da mataimakin rigistarar kotun daukaka karar ya kaiwa babban rigistarar kotun a Abuja, da yake nuni da an kammala shirin sauraren daukaka karar da Binani mai lamba CA/ YL/ EP/ AD/ GOV/ 18/2023.
Haka kuma takardar ta yi nuni da daukaka kara mai lamba CA/YL/EP/AD/SHA/19/2023, tsakanin Umar Abdullahi, APC da Calvin Kefas, PDP da kuma INEC, na dan majalisar dokokin jiha na mazabar karamar hukumar Toungo, shi ma an shirya saurarensa.
Kotun daukaka karar ta sanar da yanke hukunci kan shari’u’in biyu Rana guda (01/12/2023), tunda farko, to sai dai yanzu da ta dage bata kuma sanar da ranar da za ta saurari shari’un ba, kawo yanzu.